Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nemi amincewar Majalisar Dokokin Tarayya domin karɓar sabon bashin waje na dala biliyan 7.7, kwatankwacin Naira tiriliyan 10.79, domin taimakawa wajen cike gibin kasafin kuɗin Gwamnatin Tarayya na Naira tiriliyan 31.4 na shekarar kasafin kuɗi ta 2026.
Buƙatar, wadda ke ƙunshe cikin wasiƙar da shugaban ƙasar ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa a ranar 26 ga Oktoba, 2026, an karanta ta ne a zauren majalisar a yayin zaman ta na ranar Laraba.
Bayan gabatar da wasiƙar, Majalisar Dattawa ta miƙa buƙatar ga Kwamitinta mai kula da basussukan cikin gida da na ƙasashen waje domin nazari da kuma gabatar da rahoto kan batun.
A cikin wasiƙar, Tinubu ya bayyana cewa an ƙididdige bashin ne bisa farashin canjin kuɗin kasafin kuɗi na Naira 1,400 kan kowace dala ɗaya.
Buƙatar ta yi daidai da tanade-tanaden sashe na 21(1) da 27(1) na dokar kafa Ofishin Kula da Basussuka ta shekarar 2003, wadda ta wajabta samun amincewar majalisa kafin gudanar da duk wani aikin karɓar bashin waje.
Shugaban ƙasar ya kuma tabbatar wa ’yan majalisar cewa Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya tare da Ofishin Kula da Basussuka (DMO) za su tattauna domin samun mafi ƙarancin kuɗin ruwa da kuma wa’adin biyan bashin da ya fi dacewa, bisa yanayin kasuwar kuɗi a lokacin da za a kulla yarjejeniyar.














