Wasu ɓata-gari sun kai hari kan ayarin motocin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, da abokin takararsa, Rabiu Musa Kwankwaso, a Calabar, babban birnin Jihar Kuros Riba.
Rahotanni sun ce maharan sun yi wa motocin ayarin jifa da duwatsu da wasu abubuwa, lamarin da ya lalata wasu daga cikinsu. Sai dai Obi da Kwankwaso sun tsira ba tare da samun rauni ba.
Lamarin ya faru ne a daidai mahadar Watt Market, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa wani otel bayan ziyarar ban-girma da suka kai wa Obong na Calabar, inda daga bisani za su gudanar da taron tattaunawa da shugabanni, magoya baya da ’yan takarar jam’iyyar NDC.
Harin ya zo ne sa’o’i bayan jami’an tsaro sun hana ɓarkewar rikici tsakanin magoya bayan jam’iyyar APC mai mulki da na NDC a garin Calabar.
Kakakin rundunar ’yansandan jihar, ASP Sunday Eitokpah Akata, ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya ce an kama wani mutum mai suna Victor Edet Yellow Duke, mai shekaru 27, bisa zargin hannu a harin.
Ya kara da cewa rundunar ta kara tsaurara sa ido domin hana sake ɓarkewar rikici da tabbatar da zaman lafiya a jihar.














