Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da sake nada Farfesa Abdurrahman Abba Sheshe a matsayin babban daraktan kula da lafiya na asibitin koyarwa na Aminu Kano, da ke Kano a wa’adi na biyu kuma na karshe.
Hakan na kunshe ne acikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale ya fitar a aranar 21 ga watan Agusta, 2024.
- Kasar Sin: Shirin EU Na Kakaba Haraji Kan Motoci Masu Amfani Da Lantarki Na Kasar Sin Ya Sabawa Tarihi
- Tinubu Ya Kafa Kwamitin Tabbatar Da ‘Yancin Kananan Hukumomi A Nijeriya
An fara nada Farfesa Sheshe a matsayin babban daraktan kula da lafiya na asibitin koyarwa na Aminu Kano ne a ranar 6 ga Disamba, 2019.
Shugaban na fatan Farfesa Sheshe, zai sake sadaukar da kansa wajen inganta ka’idojin asibitin da tabbatar da samar da ingantattun kulawa ga ‘yan kasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp