Gwamnatin Tarayya ta kafa wani kwamiti mai mutum 10 da zai bibiyi tsarin bai wa kananan hukumomi cikakkiyar damar da kotun koli ta ba su a baya-bayan nan.
A ranar 11 ga watan Yulin da ya gabata ne, kotun Æ™oli ta yanke hukuncin bai wa kananan hukumomi cikakken ‘yancin cin gashin kansu da kuma zare hannun gwamnoni daga amfani da kudadensu.
- Yadda Gwamna Dauda Ya Ƙaddamar Da Asibitin Ƙauran Namoda Da Ya Inganta
- Huawei Ya Kaddamar Da Horo Game Da Tsaron Yanar Gizo Ga Jami’an Zimbabwe
Kotun kolin ta ce duk wani abu da ya shafi iko ko kuma karfin da suke da shi na tafiyar da aikin kananan hukumomi ka da gwamnoni su shiga, matakin da bai yi musu dadi ba.
A wata sanarwa da daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Segun Imohiosen ya fitar, ta ce gwamnatin ta amince da wannan kwamiti kuma za a ba shi duk karfi da gudunmawar da yake bukata.
A baya dai gwamnonin jihohi, sun yi kane-kane kan kudade da kuma karfin ikon da suke da shi, abin da ya jefa kananan hukumomi cikin matsi.
Ana ganin gwamnonin sun dauki wannan mataki ne don amfani da talaucin kananan hukumomin wajen amfani da su don biyan bukatarsu a siyasance.