Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya naɗa sabon shugaban kwamitin gudanarwar Jami’ar Bayero, ta Kano (BUK).
Ya zaɓi Air Vice Marshal Saddiq Ismaila Kaita (mai ritaya) a matsayin sabon Shugaban Kwamitin Gudanarwar jami’ar.
- Ministan Tsaron Kasar Sin Ya Nanata Shan Damarar PLA A Kan Sake Hadewar Kasar
- Zhao Leji Ya Yi Jawabi A Babban Taron Shugabannin Majalisun Kasa Da Kasa Karo Na 6
Kaita ya maye gurbin Nasiru Yusuf Gawuna, wanda yake a matsayin shugaban hukumar kula da gidaje ta ƙasa (FHA).
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce Tinubu ya sauya Gawuna ne domin ya mayar da hankali kan aikinsa a hukumar FHA.
Gawuna na hannun daman tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ne, wanda yanzu ke shugabantar hukumar FAAN.
Kafin ya yi ritaya daga Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya, AVM Kaita ya riƙe muƙamai da dama, ciki har da Daraktan Tsare-tsare a Hedikwatar Tsaro da kuma Shugaban Sashen Kirkire-Kirkire na tsaro.
Ana girmama shi saboda gudunmawar da ya bayar wajen horarwa da inganta ayyukan rundunar sojin sama.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp