Shugaban kasa, Bola Tinubu ya mika sakon taya murna ga babban editan jaridar LEADERSHIP, Azubuike Ishiekwene, murnar cika shekaru 60 da haihuwa.
Fitaccen mamba a kungiyar Editocin Nijeriya (NGE), Azu, kamar yadda aka fi sanin shi, ya yi fice a aikin jarida tsawon shekaru talatin.
- Gwamnatin Kano Ta Amince Da Biyan Bashin Albashin Ma’aikatan Tsaftar Muhalli 2,369
- Kasar Sin Ta Mayar Da Martani Ga Tattaunawar Amurka Da Rasha Kan Rikicin Ukraine
Ya yi aiki tare da manyan gidajen yada labarai da dama, ciki har da ‘The Punch’, inda ya kasance mai tace labarai, kuma marubuci a shafukan jarida na musamman, wanda yanzu haka, yake matsayin babban mai tace labarai a kamfanin LEADERSHIP Media Group.
Shugaba Tinubu, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar, ya yaba da irin hazakar da Ishiekwene ke da ita a fannin sharhi da nazari kan harkokin siyasa, tattalin arziki da halin da Nijeriya ke ciki.
Shugaban ya yaba da gudummawar da ya ke bayarwa wajen bunkasa yanayin kafafen yada labarai na Nijeriya, don haka, shugaba Tinubu na yi masa fatan alkairi a rayuwa ta gaba mai zuwa da karin kaifin basira.
Ya kuma roki Allah Madaukakin Sarki da Ya ba dan jaridan lafiya da samun biyan bukata a dukkan ayyukansa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp