Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya umarci hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ta gaggauta ficewa daga ofishin da ake ta cece-kuce a kai na Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) da ke Ikoyi, a Jihar Legas.
Shugaban ya bayar da umarnin ne a yammacin ranar Talata bayan an kawo masa rahoton rufe ofishin na EFCC.
- Yadda Kasar Sin Ke Kokarin Kawo Karshen Rikicin Ukraine A Siyasance
- ‘Yan Awaren Biyafara 30 Sun Shiga Hannun ‘Yansanda A Jihar Enugu
LEADERSHIP ta ruwaito cewa hukumar EFCC ta yi tsokaci kan kawanya da jami’an DSS suka yi wa ginin ofishinta, inda ta ce matakin barazana ce ga yaki da ta’addanci a kasar nan.
Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta ce jami’an DSS sun killace bangarenta na titin Awolowo da ke Ikoyi, ofishin Legas, inda hakan ya hana jami’ansu shiga ofishin.
A wani rubutu da hukumar EFCC ta wallafa a shafinta na sada zumunta a safiyar ranar Talata, ta ce jami’an hukumar ta Legas sun isa ofishinsu da ke lamba 15 kan titin Awolowo, Ikoyi a safiyar ranar Talata, inda jami’an DSS suka hana su shiga ofishinsu.
Sai dai kuma da ta ke mayar da martani kan zargin, hukumar ta DSS ta musanta hakan a wata sanarwa da mai magana da yawunta, Dakta Peter Afunanya ya wallafa a shafin Twitter.
Sanarwar da hukumar ta DSS ta fitar ta ce, “Ba daidai ba ne hukumar ta DSS ta hana EFCC shiga ofishinta. Ba gaskiya ba ne. Babu wata takaddama a hanyar gini mai lamba 15A da ke titin Awolowo kamar yadda kafafen yada labarai suka wallafa”.
“Babu wata hamayya tsakanin DSD da EFCC abkan komai. Labarin ba shi da tushe.”
Sai dai shugaba Tinubu, wanda ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce idan aka samu matsala tsakanin manyan hukumomin gwamnati biyu, za a warware su cikin ruwan sanyi.