Shugaba Bola Tinubu ya jinjina wa Majalisar Dokoki kan amincewa da dokar Ta-ɓaci a Jihar Ribas, inda ya bayyana cewar matakin zai taimaka wajen dawo da zaman lafiya bayan watanni da dama ana fama da rikicin siyasa.
Ya yaba wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, tare da sauran ‘yan majalisa bisa fifita tsaro sama da siyasa.
- Gidauniya Ta Jajanta Wa Waɗanda Hatsarin Tankar Gas Ya Shafa A Abuja
- Gwamnatin Nasarawa Ta Fara Aikin Sabunta Asibitoci 58 Don Inganta Lafiyar Jama’a
A cikin wata sanarwa daga mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar, ya ce Tinubu ya bayyana cewa matakin ya zama dole domin guje wa barazanar da ke tattare da kadarorin man fetur da iskar gas, tare da tabbatar da kwanciyar hankalin tattalin arziƙin ƙasa.
“Matsalar siyasa a Jihar Ribas ta kai wani mataki mai hatsari, tana barazana ga muhimman kadarorin tattalin arziƙi kuma tana lalata ci gaban da muka samu,” in ji shi.
Shugaban ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa dokar ta-ɓacin na tsawon watanni shida za ta taimaka wajen daidaita jihar da kuma samar da damar yin sulhu.
“Wannan mataki na dokar ta-ɓaci wata dama ce ta kare rayuwar al’umma, tabbatar da tsaron muhimman kadarori, da dawo da tsarin mulkin dimokuraɗiyya,” in ji Tinubu.
Shugaba Tinubu ya buƙaci dukkanin ɓangarori su mara baya ga ƙoƙarin dawo da zaman lafiya a Jihar Ribas tare da jaddada ƙudirin gwamnatinsa na bunƙasa tattalin arziƙi da haɗin kan ƙasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp