Shugaba Bola Tinubu ya yi alƙawarin ƙwato dazuzzuka da sauran yankuna a Arewa-Maso-Yamma da sauran sassan Nijeriya, yayin da yake jawabi a wata liyafa da tsofaffin shugabannin Katsina suka shirya. Ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ƙara amfani da fasahar sa ido don yaƙar ta’addanci da ƴan fashi.
A cewar sanarwar kakakin shugaban ƙasa, Tinubu ya ce: “Za mu zuba hannun jari a fasaha domin kwato dazuzzuka. Tsaro batu ne na ƙasa baki ɗaya, ba na yanki ko gunduma kawai ba.” Shugaban ya kuma yi alƙawarin inganta filin jirgin sama na Katsina domin samar da ayyukan yi.
- Gidauniyar TY Buratai Ta Yi Kira Ga Tinubu Ya Ƙarawa Ma’aikata Albashi
- Kasar Sin Ta Goyi Bayan Rawar Da Hukumar IAEA Ke Takawa Wajen Warware Batun Nukiliyar Iran Ta Hanyar Diflomasiyya
Gwamna Dikko Radda na Katsina ya bayyana cewa jihar ta kafa wani tsarin tsaro na musamman don tattara bayanan sirri, yana mai cewa inganta filin jirgin saman zai samar da ayyukan yi ga mutane 2,700. Tsohon gwamna Aminu Masari ya yaba wa shugaban saboda naɗa ‘yan asalin jihar a muƙamai mabambanta a gwamnatin tarayya.
Tinubu ya kuma yi godiya ga gwamnonin jihohin Kaduna, Jigawa, Borno, Benue, Yobe, Sokoto da Kwara da suka halarci bikin auren ‘yarsa da ƙaddamar da ayyukan gwamnati a Katsina. Ya kuma yaba wa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a matsayin mutum mai gaskiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp