Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu ya tabbatar wa da ‘yan Nijeriya shirin gwmanatin Bola Tinubu na yi wa bangaren samar da wutar lantarki garambawul, Ministan ya bayyana haka ne a sakonsa na murnar sabuwar shekara da ya aike wa ‘yan Nijeriya.
Ya kuma ce, dukkan hukumomin da ke karkashin ma’aikatar za su yi aiki tukuru wajen ganin al’ummar Nijeiya na samun wutar lantarki yadda ya kamata, za kuma su ci gaba da kara bunkasa harkokin wutar lantarki a kasar nan.
Adelabu ya kuma lura da cewa, ganin muhimmancin wutar lantarki ga tattalin arzikin kasar, a wata uku na farko da ya dare karagar mulkin ma’aikatar ya gana da dukkan masu ruwa da tsaki inda ya fito fa tsare-tsaren da za su yi amfani da su wajen samun nasarar samar wa da ‘yan Nijeriya wutar lantarki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp