Shugaba Bola Tinubu ya yi Allah-wadai da kisan mutane fiye da 40 da aka yi a Jihar Filato.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, ya bayyana baƙin cikinsa tare da jajantanwa Gwamna Caleb Mutfwang da al’ummar jihar.
- Yaƙin Neman Zaɓe A 2027: Ƙungiya Ta Nemi A Maye Gurbin Mai Magana Da Yawun Shugaban Ƙasa
- Mafarauta Sun Nemi Adalci Kan Kisan Mambobinsu A Edo
Tinubu ya buƙaci gwamnan da ya nuna ƙarfin gwiwa wajen kawo zaman lafiya mai ɗorewa.
Ya kuma roƙi shugabannin al’umma, addini da siyasa da su daina ɗaukar fansa tare da haɗa kai don zaman lafiya tsakanin ƙabilu da addinai daban-daban.
Shugaban ya ce ya umarci hukumomin tsaro da su binciko waɗanda suka aikata wannan ta’asa domin su fuskanci hukunci.
Ya kuma ce dole ne a magance tushen rikicin da ya daɗe yana addabar jihar sama da shekaru 20.
Tinubu ya tabbatar da goyon bayan Gwamnatin Tarayya ga Jihar Filato don samar da zaman lafiya, adalci da haɗin kai a tsakanin al’umma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp