Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi Balaguro a safiyar yau Litinin zuwa kasar Faransa bayan ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
A wata sanarwa da mai taimaka masa a fannin yada labarai, Tunde Rahman ya fitar a ranar Litinin, ya ce Ahmed Tinubu ya tafi birnin Paris na kasar Faransa domin gudanar da wasu muhimman taruka.
Ya kara da cewa ana sa ran dan takarar na shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC zai dawo kasar nan ba da jimawa ba.
Tun da farko kafin tafiyar tasa, Tinubu ya halarci taron kaddamar da wani littafi mai take ‘Mai girma Shugaban majalisa’ Wanda akayi taron domin bikin cika shekaru 60 da Haihuwar shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, a Abuja ranar Lahadi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp