Shugaban kasa Bola Tinubu, ya amince da rushe ma’aikatun Neja Delta da Ma’aikatar wasanni a wani yunkuri na sauya fasalin ma’aikatun tarayyar Nijeriya.
Ya bayyana matakin ne yayin taron Majalisar Zartaswa ta Tarayya (FEC), a Abuja.
- Abin Da Ya Sa Ƙasashen Duniya Suka Gina Majalisar Ɗinkin Duniya – Sakatare Janar
- Super Eagles Ta Hauro Matsayi Na 36 A Jadawalin Duniya Na FIFA
Ya sanar da sabuwar Ma’aikatar Raya Yanki a matsayin wace za ta maye gurbinsu da kula da dukkan kwamitocin raya yankin.
Wannan ya hada da hukumomi irin su Hukumar Raya Neja-Delta da Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma da Hukumar Raya Yankin Kudu Maso Yamma da Hukumar Raya Arewa maso Gabas da nufin daidaita ayyukan ci gaban yankunan a fadin kasar nan.
A halin yanzu hukumar wasanni ta kasa za ta karbi ayyukan ma’aikatar wasanni inda za ta dauki nauyin gudanarwa da bunkasa harkokin wasanni a Nijeriya.
Bugu da kari, Majalisar Zartaswan ta amince da hade ma’aikatar yawon bude ido da ma’aikatar al’adu da tattalin arziki duk a kokarin karfafawa tare da bunkasa harkokin yawon bude ido da al’adu.