Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja a ranar Lahadi zuwa Riyadh, Babban Birnin Ƙasar Saudiyya, domin halartar Taron Haɗin Gwiwar Kasashen Larabawa da Musulmai.
Za a fara taron a ranar Litinin 11 ga watan Nuwamba, tare da tattauna batutuwan da ke shafar Gabas ta Tsakiya.
- Xi Ya Gana Da Shugaban Indonesia
- Mahaifin Da Ya Kashe Jiririnsa Ɗan Kwana 3 Ya Shiga Hannun Ƴansanda
Sarki Salman da Yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman, ne suka gayyaci Shugaba Tinubu zuwa taron, wanda aka gudanar irinsa a birnin Riyadh a bara.
A yayin taron, ana sa ran Shugaba Tinubu zai yi magana kan rikicin Isra’ila da Falasdinawa, inda zai yi kira ga dakatar da yaki nan take da kuma neman samun mafita ta hanyar lumana.
Nijeriya za ta nuna goyon baya kan warware rikicin domin samun zaman lafiya a yankin.
A cewar mai ba shugaban shawara kan yada labaru, Bayo Onanuga, manyan jami’ai za su raka Shugaba Tinubu, ciki har da Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar; Mai ba da shawara kan sha’anin tsaro, Malam Nuhu Ribadu; Ministan Yada Labaru da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris; da Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), Ambasada Mohammed Mohammed.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp