A ranar Alhamis ne shugaban kasa Bola Tinubu zai kaddamar da shirin bayar da lamuni na dalibai da aka dade ana tsumayi.
Shirin, a cewar shugaban kasa, zai kawo karshen yajin aikin malamai a manyan makarantun kasar.
A ranar 12 ga watan Yunin 2023 ne shugaba Tinubu ya rattaba hannu a kan dokar samun ilimi na matakin manyan makarantu, 2023 ta zama doka don baiwa dalibai marasa karfi damar samun lamuni marar ruwa domin neman ilimi a kowace babbar jami’a ta Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp