An sake gurfanar da Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a gaban kotun koli bisa zarginsa da gabatar da kansa a matsayin shugaban kasa ba bisa ka’ida ba, lokacin da ake jiran hukuncin kotu kan gudanar da zaben shugaban kasa na 2023.
Dan takarar shugaban kasa a zaben 2019, Cif Albert Ambrose Owuru ne ya shigar da wannan kara, inda ya bukaci kotun kolin ta soke bikin rantsar da Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa a 2023.
- Hukumar Kwastam A Kano Ta Samu Kudin Shiga Naira Biliyan 6.9 A Nuwamba
- Za A Shiga Mummunar Damuwa A Gaza Idan Ba Ku Dauki Mataki Ba – Gargadi Ga Majalisar Tsaro Ta MDD
Owuru wanda ya kasance lauyan, ya ce zaben shugaban kasa da ya bayyana nasarar Tinubu, ba ya bisa ka’ida.
Karamar kotun koli mai lamba SC/667/2023, ta bayyana cewa Owuru da jam’iyyarsa ta HDP sun daukaka kara ne a yayin da wadanda ake tuhuma sun hada da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, AGF, INEC, da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Owuru yana kalubanci ayyana Tinubu a matsayin shugaban kasa da INEC ta yi a matsayin cin fuska ne ga kotun koli da kuma dokar da aka kafa. Ya kara da cewa tun da Tinubu yana cikin bangaren da ake kara a gaban kotun koli, bai kamata ya gabatar da kansa ba a matsayin shugaban kasa.
Shi dai Owuru ya tsaya takarar shugaban kasa a 2019 karkashin tutar jam’iyyar HDP, wanda ya sha kaye a hannun tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ya yi ikirarin shi ne ya lashe zaben ba Buhari ba da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta ayyana ba.
Tsohon dan takarar shugaban kasa ya bukaci kotun koli da ta hana Tinubu yin amfani da asusun tarayya har sai an kammala shari’ar da ke gaban kotu na zaben zaben 2023.
Owuru wanda ya yi ikirarin cewa shi ne wanda tsarin mulki ya tabbatar da ya lashe zaben shugaban kasa na 2019, kuma bai kamata a rantsar da wani a matsayin magajin Buhari ba har sai ya kammala wa’adinsa na shiekara hudu kamar yadda doka ta tanada.
Owuru ya dage cewa Buhari ne ya kwace masa mulki a 2019, saboda kotun koli ba ta tantance karar da ya shigar a 2019 ba, inda ya kalubalanci ayyana Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben.
Mai shari’a Inyang Edem Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja ne ya yi watsi da kararsa ta farko a ranar 30 ga watan Janairun 2023, lamarin da ya sa ya koma kotun daukaka kara.
Kotun daukaka kara da ke Abuja a nata bangaren, ranar 25 ga watan Mayu a hukuncin da mai shari’a Jamil Tukur wanda ya jagoranci alkalan kutun mutum uku ya ki dakatar da bikin rantsar da Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu.