- Har Yanzu Atiku Bai Dawo Hayyacinsa Ba Bayan Shan Kaye — Fadar Shugaban Kasa
- Idan Tinubu Ya Isa Ya Bari Kotu Ta Yi Adalci — Atiku
Har yanzu dai tsugune ba ta kare ba game da zaben shugaban kasar da ya bai wa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu damar hawa kujera, inda a wannan makon bangarorin da ke ja-in-ja a kotu kan sahihancin zaben suka kwaba wa juna magana.
Fadar shugaban kasa ta yi watsi da ikirarin da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi kan zargin wakilan shugaban kasa, Bola Tinubu da jam’iyyar APC na tursasa bangaren shari’a don a murde gaskiyar lamari kan kalubalantar nasarar sakamakon zaben shugaban kasa na 2023 a kotu.
Da yake mayar da martani kan zargin, mai bai wa shugaban kasa shawara kan ayyukan na musamman da suka shafi sadarwa da tsare-tsare, Dele Alake ya bayyana cewa fadar shugaban kasa fa tana zargin cewa har yau dan takarar jam’iyyar PDP bai farfado daga mugun kaye da ya sha a zaben shugaban kasa.
Ya dai zargin shi da kokarin yi wa bangaren shari’a zagon kasa, wanda Tinubu ba zai taba yin haka ba.
Ya kara da cewa: “Mun yi nazari kan kalaman tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata, Alhaji Atiku Abubakar mu ka ga babu abin da ke ciki sai abun dariya.
“A bayyane yake cewa jam’iyyar APC ta lallasa PDP wanda a yanzu Tinubu shi ne shugaban kasa, wanda har yanzu tsohon mataimakin shugaban kasar bai gama murmurewa daga kaduwa na shan kaye ba, don haka yunkurin da ake yi na tayar da kayar baya a halin yanzu, ya saba wa tunani da kuma hankalin Dan’adam.
“A cikin wannan furucin na rashin tunani da ma’ana, Alhaji Atiku ya zargi gwamnatin APC mai mulki da shirya zagon kasa ga bangaren shari’a ba tare da bayar da wata kwakkwarar shaida ba. Baya ga zage-zage da kareyayi da ke kunshe a cikin sanarwar manema labarai da ya fitar, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku bai gabatar da wata gamsasshiyar hujja da za ta goyi bayan ikirarinsa kan yadda gwamnatin Shugaba Tinubu da jam’iyyar APC ke neman yi wa shari’a zagon kasa.
“Idan har tsohon mataimakin shugaban kasa ya yi imani da tsarin dimokuradiyya da kuma tsaftar bangaren shari’a, ba zai taba yin irin wannan zage-zage da nufin tozarta wani muhimmin bangaren gwamnati da ya kamata ya zama ginshikin dimokuradiyyarmu ba.
“Ba tare da jin kunya ba ya yi wannan ikirari na tursasawa da kuma yi wa bangaren shari’a zagon kasa a daidai lokacin da lamarin yake gaban kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa.
“Idan aka tabo maganar gwagwarmayar tabbatar da dimokuradiyya da akidar dimokuradiyya, dokar Nijeriya ta bai wa bangaren shari’a ‘yanci, wanda dole Shugaba Tinubu da Atiku su tsayu a kai. A lokacin da Shugaba Tinubu ke gwagwarmayar samar wa bangaren shari’a ‘yanci da kuma tabbatar da tsaftar doka a matsayin ginshikin samar da shugabanci nagari a matsayinsa na gwamnan Jihar Legas a tsakanin 1999 zuwa 2007 a karkashin gwamnatin PDP, Atiku yana ina.
“Shugaba Tinubu ya yi amfani da doka da shari’a ta hanyar samun nasarar kalubalantar tsattsauran ra’ayi da munanan hukunce-hukunce na gwamnatin tarayya karkashin jam’iyyar PDP wanda ta tauye hakkin jihohi a matsayin gwamnatin tarayya. Jihar Legas karkashin jagorancin Tinubu ta yi nasara a kan kararraki 13 a kotun koli a kan gwamnatin PDP da ke karkashinta a wancen lokaci.
“Babu wani shugaban da ke da wannan hazaka da kishi a matsayin mai fafutukar tabbatar da doka da oda, ‘yancin cin gashin kai irin na Shugaba Tinubu da zai yi tunanin zagon kasa ga bangaren shari’a kamar yadda Alhaji Atiku ya yi zargin.
“Shugaba Tinubu ya lashe zabe na gaskiya da gaskiya. Ranar 25 ga Fabrairu, 2023, zaben shugaban kasa da aka yi shi ne zabe mafi inganci da aka taba gudanarwa a Nijeriya tun 1999.
“Shugaba Tinubu da jam’iyyar APC ba su da wani dalili na durkusar da bangaren shari’a domin samun damar yin nasara a wani shari’a.
“Lauyoyinsa da na APC sun gabatar da hujjoji na kare sakamakon zaben kuma muna da tabbacin kotu za ta yanke hukunci ba tare da nuna son kai ba bisa dalilai na shari’a da shaidun da ke gabanta, ba wai ya yi ta zage-zage marasa tushe ba.
“Ya kamata Atiku ya girmama bangaren shari’a wajen gudanar da ayyukanta ba tare da tsangwama ba. Rashin adalci ne ga tsohon mataimakin shugaban Nijeriya ya dunga yin wannan kalamu kuma ya kamata ya dakatar da su.”
A nashi bangaren kuwa, dan takarar jam’iyyar PDP a zaben sshugaban kasa na ranar 25 ga Fabrairu, Alhaji Abubakar Atiku ya bayyana cewa idan Shugaban kasa Tinubu ya isa ya bari kotu ta yi adalci kan zaben shugaban kasa.
A jawabin karshe da Atiku da PDP suka yi a rubuce a takardar da suka shigar na kalubalantar ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da babban lauyansu, Cif Chris Uche ya jagoranta, Atiku ya ce zaben na ranar 25 ga watan Fabrairu shi ne mafi muni a tarihin zabe a Nijeriya.
Masu shigar da kara sun bayyana haka ne a cikin rubutaccen jawabinsu na karshe cewa an sauya sakamakon zabe da ‘yan Nijeriya suka kada, duk da kafa sabuwar dokar zabe da bullo da sabbin fasahohin zamani da aka yi alkawarin tabbatar da gaskiya da dimbin kudaden dsa aka kashe, wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayar da tabbaci gudanar da sahihin zaben, amma hakan ya ci tura.
A cewar Atiku, bisa uzurin da INEC ta bayar na matsalar na’urorin da aka samu, an samu damar tafka magudi ta hanyar sauya sakamakon zabe domin Tinubu ya yi nasara.
Atiku ya ce: “Tsarin yin amfani da fasahar na’urar tantance masu zabe da aka yi amfani da shi ya gudana a duk fadin kasar nan, amma aka kasa yin amfani da shi wajen bayyana sakamakon zabe.”
Uche ya bayyana cewa, INEC ta ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa duk da bai cika ka’idojin da kundin tsarin mulki ya tanada ba na samun kasa da kashi daya bisa hudu na kuri’un da aka kada a Babban Birnin Tarayya Abuja.
Atiku da jam’iyyarsa sun shaida wa kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa cewa, bisa tsarin mulkin kasar, bai kamata Tinubu ya tsaya takarar shugabancin Nijeriya ba, bisa la’akari da hukuncin da aka yanke masa na kwace dala 460,000 kan laifukan da suka shafi muggan kwayoyi a Amurka da kuma rike da takardar shaidar zama dan kasa biyu, Nijeriya da Guinea, baya ga gabatar da takardun bogi INEC.
Bayan da INEC ta samun umarnin kotu na sake fasalin na’urar tantance masu kada kuri’a (BBAS) da aka yi amfani da su wajen zaben, masu shigar da kara sun yi ikirarin cewa hukumar zaben ta wanke dukkanin na’urorin BBAS daga bayanan kamar yadda aka tabbatar a wasikarsu mai kwanan wata 17 ga Mayu, 2023.
Domin tabbatar da shari’ar, Uche ya ce, masu shigar da kara sun gabatar da shaidu 27 tare da gabatar da takardu da dama, inda suka bayyana cewa, bisa ga alkawarin INEC ta yi na bayyana sakamakon zabe a na’ura tun daga rumfunan zabe hakan bai samu ba.
Atiku da PDP sun gabatar da batutuwa guda hudu a gaban kotu kotu, wanda suka hada da ko dai bayyan Tinubu a matsayin wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasa bai inganta ba, saboda rashin bin ka’idojin dokar zabe ta 2002 kan bayyana sakamakon zaben ta na’ura domin tattarawa da tabbatarwa.
Ko an bi tsarin doka wajen ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa, domin bai samu kashi daya bisa hudu na kuri’un da aka kada a Babban Birnin Tarayya Abuja kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
Ko dai a soke nasarar Tinubu a karkashin dokar da kundin tsarin mulkin kasar ya tanada na tsayawa takarar shugaban kasa, la’akari da hukuncin laifukan da suka shafi muggan kwayoyi, da kuma gabatar da takardar kasa biyu da kuma mika takardar shaidar jabu ga INEC.
Ko kuma INEC ta yi kuskure wajen bayyan Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa kasancewar bai samu mafi yawan kuri’un da aka jefa a zaben ba.