Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ƙaddamar da sabon haraji kan kayayyakin da ake shigowa da su Amurka daga ƙasashen duniya.
Wannan mataki zai shafi ƙasashe da dama, inda wasu suka ce za su mayar da martani ta hanyar ɗora wa Amurka haraji iri ɗaya.
- Shugaba Putin Ya Gana Da Ministan Harkokin Wajen Sin
- Yadda Rasuwar Galadima Abbas Ta Haɗa Kawuna ‘Yan Siyasar Kano Masu Hamayya Da Juna
Sabon harajin zai fara daga 10 zuwa sama, kuma ya shafi duk wasu kayayyaki daga ƙasashen da ba su cikin yarjejeniya ta USMCA, wadda ta haɗa Amurka, Mexico da Kanada.
A Turai, harajin zai kai 20, yayin da Switzeland za ta fuskanci haraji har 50.
Hakazalika, an ce haraji mai tsauri zai fara aiki daga 9 ga wata. Afrilu kan ƙasashe 60 da Amurka ke zargi da rashin adalci a cinikayya.
Harajin kan motocin da ake shigo da su Amurka daga ƙasashen waje zai kai 25, wanda zai fara aiki daga ƙarfe 12 na daren ranar Laraba.
Shugaba Trump ya ce matakin na nufin kare tattalin arziƙin Amurka da muradun ‘yan ƙasarta.
Ana sa ran ƙasashe kamar Tarayyar Turai, China, Japan, da Koriya ta Kudu za su mayar da martani cikin gaggawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp