Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bai wa Rasha wa’adin kwanaki 50 ta kawo ƙarshen yaƙin da tabke yi da Ukraine, ko kuma ta fuskanci sabon takunkumi masu tsauri.
Ya ce idan ba a cimma yarjejeniyar zaman lafiya ba, za a saka haraji na kashi 100 cikin 100 kan kayayyakin Rasha da ma ƙasashen da ke ci gaba da kasuwanci da ita, domin ƙara matsin lamba ga Moscow.
- Sojoji Sun Daƙile Satar Mai, Sun Kama Mutane 50 A Neja Delta
- Sin Na Maraba Da ’Yan Jaridar Duniya Da Su Halarci Bikin Cika Shekaru 80 Da Cimma Nasarar Yakin Kin Harin Japan Da Na Tafarkin Murdiya
Trump ya kuma sanar da sabuwar yarjejeniya da ƙungiyar tsaro ta NATO.
A ƙarƙashin wannan yarjejeniya, NATO za ta sayi makamai masu darajar biliyoyin daloli daga Amurka ciki har da garkuwar rokoki na Patriot domin aike su zuwa Ukraine cikin gaggawa.
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya bayyana godiyarsa ga Trump bisa wannan taimako.
Duk da haka, dakarun Rasha na ci gaba da kai hare-hare.
Sun ce sun ƙwace ƙarin yankuna a gabashin Ukraine tare da kashe fararen hula.
A birnin Kyiv kuwa, Zelensky ya ba da shawarar sauya Firaminista domin ƙara ƙarfafa gwamnati.
Wasu ’yan Ukraine sun nuna farin ciki da zuwan makaman, duk da cewa sun zo a makare.
Wani soja ya ce makaman Patriot za su taimaka wajen kare iyalansu daga hare-haren ta sama da Rasha ke kai musu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp