A wani mataki da ya zo ba zato ba tsammani, shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da dakatar da wasu haraji da ya saka wa kayayyakin da ake shiga da su ƙasar da su daga ƙasashen duniya.
Wannan dakatarwar ba ta shafi China ba, domin ya ƙara haraji kan kayayyakin da ake shiga da su ƙasar daga can.
- Sin Ta Kara Wasu Kamfanonin Amurka 12 Cikin Jerin Wadanda Ta Dakatar Da Fitar Musu Da Wasu Kayayyaki Daga Kasar Sin
- Yadda Kasashen Afirka Za Su Iya Rage Illar Harajin Amurka
A cewar saƙon da Trump ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, ya ce za a rage harajin kan kayayyakin waje zuwa kashi 10, amma kayan da ke zuwa daga China za su fuskanci ƙarin haraji zuwa kashi 125.
Trump ya zargi China da nuna rashin adalci da girmamawa ga Amurka, yana mai cewa ƙasar na cin gajiyar kasuwanci ba tare da daidaito ba.
Tun kafin wannan mataki, China ta mayar da martani da ƙara haraji kan kayayyakin Amurka zuwa kashi 84, inda ta zargi gwamnatin Trump da amfani da dabarun “zare ido” da matsin lamba wajen nuna ƙarfi a harkokin cinikayya da ƙasashen duniya.
Wannan rikicin haraji ya faro ne tun shekarar 2018, lokacin da Trump ya fara ƙaƙaaba wa China da wasu ƙasashe haraji mai tsanani kan kayayyakin da ake shiga da su Amurka, a wani yunƙuri na kare masana’antu da ayyukan yi a cikin gida.
Sai dai masana tattalin arziƙi sun ce wannan mataki zai iya kawo tasiri ga farashin kayayyaki a Amurka da kuma haifar da sabuwar ɓaraka a dangantakar cinikayya tsakanin manyan ƙasashen duniya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp