Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya sanya hannu kan sabuwar dokar da ta hana ‘yan wasan da sukai sauyin jinsi (transgender) shiga wasannin mata. Ya bayyana cewa wannan dokar zata kawo ƙarshen “cece ku ce da ake yi kan wasannin mata” tare da tabbatar da kariya ga ‘yan wasa mata daga fuskantar rashin adalci.
A dokar Trump na neman a dakatar da makarantu daga samun tallafin gwamnati idan suka bari ‘yan wasan transgender su taka leda a ƙungiyoyin mata.
- Sin Ta Sanar Da Daukar Matakan Mayar Da Martani A Kan Karin Harajin Amurka
- Sin Za Ta Mai Da Martani Kan Dukkanin Cin Zalin Ciniki Da Aka Yi Mata
Haka zalika, Trump ya shirya matsa wa ƙungiyar wasannin Olympics ta duniya (IOC) don su sauya dokokinsu game da ‘yan wasan transgender kafin gasar Olympics ta Los Angeles a shekarar 2028.
Bugu da kari, Trump ya umarci hukumar tsaron cikin gida ta ƙasa da ta ƙi amincewa da neman visa daga ‘yan wasan da suka yi ikirarin cewa su mata ne don shiga wasanni
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp