ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, November 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Trump Ya Zabi Mai Shekaru 39 A Matsayin Mataimakinsa

by Sadiq
1 year ago
Trump

Tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump ya zabi Sanata James David Vance na Jihar Ohio, a matsayin mataimakinsa a takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar Republican.

A ranar Litinin Trump mai shekaru 78 ya zabi Vance mai shekaru 39 a matsayin abokin tafiyarsa a zaben 2024 wanda za a yi a ranar 5 ga watan Nuwamba.

  • Sin Ta Fadada Manufar Yada Zango A Kasar Ba Tare Da Biza Ba Zuwa Karin Tashoshi
  • Tsadar Rayuwa: Gwamnatin Tarayya Ta Fara Rabon Tirelolin Shinkafa 740 A Fadin Nijeriya 

Baya ga shi Vance, a baya, an bayyana mutum biyu da ake tunanin Trump zai dauka ciki har da Sanata Marco Rubio na Jihar Florida da gwamnan Jihar North Dakota Doug Burgum.

ADVERTISEMENT

Trump, ya sanar da zabinsa da aka jima ana dako a babban taron jam’iyyar Republican na kasa da aka fara a Milwaukee da ke Jihar Winsconsin.

Dukkanin wakilan da suka halarci babban taron na ‘yan Republican daga jihohin Amurka sun jaddada Trump a matsayin dan takararsu a zaben shugaban kasa, inda ya samu wakilai sama da 1,215 adadin da ake bukata dan takara ya samu.

LABARAI MASU NASABA

Tsohon Gwamnan Anambra, Willie Obiano, Ya Rasu Yana Da Shekaru 70

Musulmin da Aka Kashe  A Zamfara, Katsina Da Sokoto Sun Ninka Na Kiristoci A Tsakiyar Najeriya: MACBAN

Gangamin na ‘yan Republican na zuwa ne kwanaki biyu bayan da Trump ya tsallake rijiya da baya inda wani dan bindiga ya yi yunkurin hallaka shi yayin gangamin yakin neman zabe a Pennsylvania a ranar Asabar.

An haifi Vance ne a garin Middleton da ke Jihar Ohio a ranar 2 ga watan Agustan 1984.

Ya kammala karatun lauyansa a makarantar koyon aikin lauya ta Yale, ya kuma taba aiki da rundunar sojin Amurka bayan da ya kammala karatun sakandare.

An fara zaben Vance a matsayin Sanata ne a 2022 bayan da ya doke abokin hamayyarsa na jam’iyyar Democrat Tim Ryan.

A 2016, ya kasance daya daga cikin masu sukar Trump, amma ya sauya akalar kalamansa a lokacin da ya tashi yin takararsa ta farko a 2022.

Ya yi aure a 2014, kuma yana da ‘ya’ya uku.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tsohon Gwamnan Anambra, Willie Obiano, Ya Rasu Yana Da Shekaru 70
Da ɗumi-ɗuminsa

Tsohon Gwamnan Anambra, Willie Obiano, Ya Rasu Yana Da Shekaru 70

November 14, 2025
Musulmin da Aka Kashe  A Zamfara, Katsina Da Sokoto Sun Ninka Na Kiristoci A Tsakiyar Najeriya: MACBAN
Manyan Labarai

Musulmin da Aka Kashe  A Zamfara, Katsina Da Sokoto Sun Ninka Na Kiristoci A Tsakiyar Najeriya: MACBAN

November 14, 2025
Kotu Ta Yanke Wa Mutum 4 Hukuncin Kisa Kan Kashe Wani Makanike A Kano
Manyan Labarai

Kotu Ta Yanke Wa Mutum 4 Hukuncin Kisa Kan Kashe Wani Makanike A Kano

November 14, 2025
Next Post
Ku Tabbatar Kun Bai Wa Mabukata Shinkafar Da Aka Ba Ku – Gwamnatin Tarayya Ga Gwamnoni 

Ku Tabbatar Kun Bai Wa Mabukata Shinkafar Da Aka Ba Ku - Gwamnatin Tarayya Ga Gwamnoni 

LABARAI MASU NASABA

Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya

Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya

November 14, 2025
NAHCON Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Da Zai Kula Da Shafin Nusuk Masar Na Hajjin 2026

NAHCON Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Da Zai Kula Da Shafin Nusuk Masar Na Hajjin 2026

November 14, 2025
NSCDC Ta Cafke Mutum Biyu Bisa Zargin Satar NAPEP Da Safarar Miyagun Kwayoyi A Kano

NSCDC Ta Cafke Mutum Biyu Bisa Zargin Satar NAPEP Da Safarar Miyagun Kwayoyi A Kano

November 14, 2025
Gwamnan Gombe Ya Gabatar Da Naira Biliyan 535.69 A Matsayin Kasafin 2026

Gwamnan Gombe Ya Gabatar Da Naira Biliyan 535.69 A Matsayin Kasafin 2026

November 14, 2025
Sin Za Ta Mayar Da Martani Idan Har Japan Ta Aiwatar Da Matakin Da Bai Dace Ba

Sin Za Ta Mayar Da Martani Idan Har Japan Ta Aiwatar Da Matakin Da Bai Dace Ba

November 14, 2025
Tinubu Ya Zuba Naira Tiriliyan 1.5 Don Bunkasa Noma Da Kayan Aiki Na Zamani

Tinubu Ya Zuba Naira Tiriliyan 1.5 Don Bunkasa Noma Da Kayan Aiki Na Zamani

November 14, 2025
Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Saman Yaki Na Sichuan Ya Fara Gwajin Sufuri A Karon Farko

Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Saman Yaki Na Sichuan Ya Fara Gwajin Sufuri A Karon Farko

November 14, 2025
Rashin Daukar Tsauraran Matakai Na Iya Durkusar Da Bangaren Noma – Shehu Galadima

Dalilin Asusun NADF Na Yin Hadaka Da Gwamnatin Jihar Jigawa

November 14, 2025
Xi Jinping Ya Gana Da Sarkin Thailand

Xi Jinping Ya Gana Da Sarkin Thailand

November 14, 2025
BUK Za Ta Kafa Cibiyar Horas da Aikin Jarida da Sabbin Kafofin Sadarwa Na Zamani

BUK Za Ta Kafa Cibiyar Horas da Aikin Jarida da Sabbin Kafofin Sadarwa Na Zamani

November 14, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.