Jami’ai a fannin gine-gine a kasar nan sun bayyana cewa, samun hauhawan farashin kayan yin gini, na janyo fannin tarnaki.
Shugaban karamar hukumar Agboyi-Ketu da ke a jihar Legas Dele Oshinowo ya bayyana hakan a kwanan baya a taron manema labarai a yankin.
- Amurka Ta Zama Babban Cikas Ga Dakile Yakin Gaza Bayan Da Ta Hau Kujerar Na Ki
- Blinken: Idan Ba Ka Da Karfi, Za A Cinye Ka
Dele ya danganta hauhawan farashin kayan na yin gini akan abubuwa da dama da suka hada da, samun sauyin kan farashin kayan, rashin tsaro, rashin samun kwararrun a fannin da sauransu.
Don a lalubu da mafita kan wadannan matsalolin Dele ya ce, ana bukatar bangaren gwamnati da masu zama kansu, su kawo fannin daukin da ya dace.
Ya kara da cewa, bin ka’ida, zuba jari a fannin gine-gine da samar da shirye-shiryen bayar da horo, za su taimaka matuka wajen magance hauhawan farashin na kayan gini a kasar nan.
Dele ya yi nuni da cewa, kirkiro da kyakyawan yanayi na yin kasuwanci, tabbatar da gaskiya, za su taimaka waien janyo hankalin masu son zuba jari a fannin na gine-gine, wanda hakan zai kuma taimka wajen tsadar farashin kayan na gine-gine.
Shi ma wani masani a fannin gine-gine Olorunyomi Alatise ya sanar da cewa, kara farashin kayan gini da masu saraffa su ke yi ne ke haifar da tsada a fannin gini.
Ya kara da cewa, tsadar kayan aikin na janyo tsaiko wajen gudanar da akin ginin tare da kuma shafar kasafin kudin da aka yi za a kashe don yin ginin.
A cewarsa, tsadar za ta kuma iya zamo wa masu gina gidaje don sayar wa cikas wajen samun kudaden da za su zuba don yin gine-ginen.
Ya ci gaba da cewa, tsadar ta kayan ginin za ta kima iya janyo wa a yi gini maras inganci.
A bisa kokarin da ake yi na samar da sauki kan hauhawan farashin Siminti da sauran kayan gini don a samar da gidaje masu saukin kudi a kasar nan, a ranar Alhamis data gababa, Ministan gidaje da raya birane Ahmed Dangiwa, ya yi wata gana wa da masu sarrafa Simintin da sauran kayan gine-gine.
Bugu da kari, Dele ya kuma kaddamar da aiki na gaba da mulkinsa ya kikiro da shi don inganata rayuwar alummar karamar hukumar ta Agboyi-Ketu.
Ya kara da cewa, aikin zai mayar da hankali ne wajen tsarin gina gidaje, gina titina, yin zirga -zirga da gyarn gine-ginen hukumar.
Ya sanar da cewa, “ Muna daf da kaddamar da sassan gidajen kwana guda 170 da su dauki dakunan kwana bi biyu da kuma wasu sasaan gine-gine guda 102 da za su dauki dakunan kwana guda hudu da jimlarsu takai guda 271.
Kazalika ya ce, za a kuma samar wa da mazuna yankin da wutar lantarki da za ta kai awa 18 suna morewa”.
Sai dai, Dele ya ce, farashin gidajen ya karu daga Naira miliyan 15.5 zuwa Naira miliyan16.5, inda ya kara da cewa, akwai kuma gidajen da kudinsu ya kai Naira miliyan 18.5 wadanda suka kai kimanin kashi 80 wadanda tuni, ma’aikata da sauran wasu mazuna yankin suka siya suka kuma shiga cikinsu.
Dele ya sanar da cewa, aikin da zai yi na gaba shi ne, gina sassa 248 da su dauki dakunan kwana hudu da sauransu.
Ya ce, karamar hukumar ta Agboyi Ketu, ta yi hadaka da kafanonin Google da na Microsoft domin a bayar da horo ga mazauna yankin kan fasahar zamani ta ICT.