ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsadar Kayan Aiki Na Shafar Shirin Samar Da Gidaje A Nijeriya

by Abubakar Abba
3 years ago
Gidaje

Jami’ai a fannin gine-gine a kasar nan sun bayyana cewa, samun hauhawan farashin kayan yin gini, na janyo fannin tarnaki.

Shugaban karamar hukumar Agboyi-Ketu da ke a jihar Legas Dele Oshinowo ya bayyana hakan a kwanan baya a taron manema labarai a yankin.

  • Amurka Ta Zama Babban Cikas Ga Dakile Yakin Gaza Bayan Da Ta Hau Kujerar Na Ki
  • Blinken: Idan Ba Ka Da Karfi, Za A Cinye Ka

Dele ya danganta hauhawan farashin kayan na yin gini akan abubuwa da dama da suka hada da, samun sauyin kan farashin kayan, rashin tsaro, rashin samun kwararrun a fannin da sauransu.

ADVERTISEMENT

Don a lalubu da mafita kan wadannan matsalolin Dele ya ce, ana bukatar bangaren gwamnati da masu zama kansu, su kawo fannin daukin da ya dace.

Ya kara da cewa, bin ka’ida, zuba jari a fannin gine-gine da samar da shirye-shiryen bayar da horo, za su taimaka matuka wajen magance hauhawan farashin na kayan gini a kasar nan.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Taron Bikin Maulidi Ya Gudana A Unguwar Mile 12 A Legas

NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba

Dele ya yi nuni da cewa, kirkiro da kyakyawan yanayi na yin kasuwanci, tabbatar da gaskiya, za su taimaka waien janyo hankalin masu son zuba jari a fannin na gine-gine, wanda hakan zai kuma taimka wajen tsadar farashin kayan na gine-gine.

Shi ma wani masani a fannin gine-gine Olorunyomi Alatise ya sanar da cewa, kara farashin kayan gini da masu saraffa su ke yi ne ke haifar da tsada a fannin gini.

Ya kara da cewa, tsadar kayan aikin na janyo tsaiko wajen gudanar da akin ginin tare da kuma shafar kasafin kudin da aka yi za a kashe don yin ginin.

A cewarsa, tsadar za ta kuma iya zamo wa masu gina gidaje don sayar wa cikas wajen samun kudaden da za su zuba don yin gine-ginen.

Ya ci gaba da cewa, tsadar ta kayan ginin za ta kima iya janyo wa a yi gini maras inganci.

A bisa kokarin da ake yi na samar da sauki kan hauhawan farashin Siminti da sauran kayan gini don a samar da gidaje masu saukin kudi a kasar nan,  a ranar Alhamis data gababa, Ministan gidaje da raya birane Ahmed Dangiwa, ya yi wata gana wa da masu sarrafa Simintin da sauran kayan gine-gine.

Bugu da kari, Dele ya kuma kaddamar da aiki na gaba da mulkinsa ya kikiro da shi don inganata rayuwar alummar karamar hukumar ta Agboyi-Ketu.

Ya kara da cewa, aikin zai mayar da hankali ne wajen tsarin gina gidaje, gina titina, yin zirga -zirga da gyarn gine-ginen hukumar.

Ya sanar da cewa, “ Muna daf da kaddamar da sassan gidajen kwana guda 170 da su dauki dakunan kwana bi biyu da kuma wasu sasaan gine-gine guda 102 da za su dauki dakunan kwana guda hudu da jimlarsu takai guda  271.

Kazalika ya ce, za a kuma samar wa da mazuna yankin da  wutar lantarki da za ta kai awa 18 suna morewa”.

Sai dai, Dele ya ce,  farashin gidajen ya karu daga Naira miliyan 15.5 zuwa Naira miliyan16.5, inda ya kara da cewa, akwai kuma gidajen  da kudinsu ya kai Naira miliyan 18.5 wadanda suka kai kimanin kashi 80 wadanda tuni, ma’aikata da sauran wasu mazuna yankin suka siya suka kuma shiga cikinsu.

Dele ya sanar da cewa, aikin da zai yi na gaba shi ne, gina sassa 248 da su dauki dakunan kwana hudu da sauransu.

Ya ce, karamar hukumar ta Agboyi Ketu, ta yi hadaka da kafanonin Google da na Microsoft domin a bayar da horo ga mazauna yankin kan fasahar zamani ta ICT.

Gidaje
Abubakar Abba
+ postsBio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood

MASU ALAKA

Yadda Taron Bikin Maulidi Ya Gudana A Unguwar Mile 12 A Legas
Tattalin Arziki

Yadda Taron Bikin Maulidi Ya Gudana A Unguwar Mile 12 A Legas

September 4, 2026
NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
Tattalin Arziki

NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba

September 4, 2026
NPA Ta Tabbatar Da Maido Da Manyan Kayan Aikin Hukumar Wuta Ta Neja Delta —Babbar Manaja
Tattalin Arziki

NPA Ta Tabbatar Da Maido Da Manyan Kayan Aikin Hukumar Wuta Ta Neja Delta —Babbar Manaja

August 28, 2026
Next Post
Jihar Kaduna Ta Fara Ƙwaƙƙwaran Bincike Kan Yadda Lassa Ta Kashe Mutane A Asibitin Sojoji

Jihar Kaduna Ta Fara Ƙwaƙƙwaran Bincike Kan Yadda Lassa Ta Kashe Mutane A Asibitin Sojoji

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.