A kokarinsa na kawo tallafi ga talakawa da marasa karfi na jihar Kaduna, gwamnan jihar, Sanata Uba Sani ya ce gwamnatinsa za ta kashe zunzurutun kudi har Naira biliyan 11.4 wajen rabon kayayyakin tallafi na biyu ga ‘yan jihar.
Gwamna Sani ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a yayin kaddamar da rabon kayan tallafin kashi na biyu ga al’ummar jihar Kaduna.
- Wasu Mahara Sun Lalata Layin Dogo Na Jirgin Ƙasa A Jihar Kaduna
- Gwamna Uba Sani Ya Ƙaddamar Da Ginin Kamfanin Haɗa Magunguna Na AMA-MED A Kaduna
Gwamnan ya ce, “Ina mai farin cikin sanar da ku cewa, a yau za mu fara rabon kayan abinci da suka hada da shinkafa da masara har tirela 128 wanda kudinsu ya kai Naira biliyan 3.4 ga talakawa, marasa karfi da mabukata na jihar Kaduna. Muna harin gidaje 200,000 da ke kunshe da mutane kimanin 1,000,000 domin cin gajiyar shirin.
Gwamnan ya kara da cewa, gwamnatinsa ta gano cewa, kawar da talauci a yankunan karkara shi ne babbar hanyar bude kofar ci gaban tattalin arziki a jihar Kaduna.