Hukumar Kwastam reshen jihar Kano, ta ce ta cafke wasu manyan motoci guda hudu dauke da kayan abinci a kokarin hukumar na magance matsalar masu fitar da abinci zuwa ketare.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Saidu Nuradeen, ya fitar ranar Talata a Kano.
- ‘Yan Kasuwar Kano Sun Nemi Gwamnati Ta Kawo Dauki Kan Halin Da Kasuwannin Ke Ciki
- Mbappe Ya Amince Ya Koma Real Madrid Akan Kwantiragin Shekaru 5 A Karshen Kakar Wasa Ta Bana
Ya ce jami’an hukumar sun kama motocin makare da kayan abinci da aka yi niyyar fitarwa ba bisa ka’ida ba a kan iyakar Hadejia zuwa Taura zuwa Ringim a Jigawa.
Acewarsa, kayayyakin da ake jigilar sun hada da kwalin busasshen kifi – manya da kanana guda 1,505, buhunan shinkafa iri-iri guda 17 da buhunan wake guda biyu.
Ya kara da cewa, cafke kayayyakin ya nuna jajircewa da kokarin da Hukumar ke yi na aiwatar da manufar rufe iyakokin kasar da nufin kare tattalin arzikin kasar da tabbatar da samar da abinci acikin gida.
A yayin da ya bukaci jama’a da su samar da sahihin bayanai domin samun damar dakile fasa kwaurin, Nuradeen ya kara jaddada kudurin hukumar na dakile ayyukan da basu inganta ba domin kare masana’antu na cikin gida da kuma inganta samar da abinci.