A yayin da Nijeriya ke ci gaba da fusknatar kalubalen tattalin arziki da kuma hauhawan farashin kaya wanda wasu ke ganin, shi ne ma fi tsananai a cikin shekara 17 da suka wuce, hakan ya kuma shafi masu sana’ar kiwata Kajin gidan gona, inda wasu masu sana’ar a jihar kasno wadanda tsadar ‘yan tsakin da abincinsu, ta tilasata su dakatar da sana’ar.
Wani mai yin sana’ar a jihar Bala Idris ya bayyana cewa, wasu daga cikin masu sanar’ar a jihar ta Kano sun durkushe saboda wannan matsalar, inda wasu da daman masu sana’ar ke ta fafutura neman mafita, saboda irin wannan kalubalen da fannin ke fuskanta a jihar.
- Adabin Zamanin Da Na Sin (3)
- Ana Baje Kolin Shirye-Shiryen CMG A Taron Kafofin Watsa Labaran Kasa Da Kasa Karo Na Farko
Wasu masu sana’ar sun ce, farashin na abincin Kaji da kuma farashin ‘yan tsakin ya fi tashi a cikin watan Nuwamba zuwa Disamba, amma a bana,tashin farashin ya yi kamari matuka.
Wasu masu ruwa da tsaki a fannin da ke jihar Yakubu Ibrahim, wanada ke da gonar kiwon Kajin da ake kira ‘Albarka’ ya bayyana cewa, saboda wadannan kalubalen a yanzu, ba ya iyan sana’ar kamar da, inda ya kara da cewa, a da, ba su taba fuskantar wannan kalubalen ba.
Ibrahim ya ce, akwai abubuwa da dama da suka jawo haka, wadanda suka hada da tsadar Kajin da abincinsu, inda hakan ya jawo masu sana’ar ke fice daga cikinta.
Ya kara da cewa, ana kuma fuskantar kalubalen masu yin kyankyasar ‘yan tsakin a jihar, inda ya kara da cewa, daukacin ‘yan tsakin ana shigo da su ne daga kudancin kasar nan domin akasari ba a cika samun kamfanonin da ke yin kyankyasar ‘yan tsakin a jihar ba.
Ibrahim ya ce, masu kiwon Kaji da ake kira da ‘Broilers’ a Ingilishi, su ne suka fi fuskantar wannan kalubalen domin farashinsu ya tashi matuka wanda kuma ba a taba ganin hakan ba.
A cewarsa, a baya hakan ya fi aukuwa a lokacin bukukuwan karshen shekara lokacin gudanar da bikin Kirismeti, domin masu kiwata su na ci gaba da kiwon su ne har tsawon wata uku ko hudu.
“Masu kiwon Kaji da ake kira ‘Broilers’ a jihar, su ne suka fi fuskantar wannan kalubalen domin farashin su ya tashi matuka wanda kuma ba a taba ganin hakan a ba yaba”.
Bincike ya nuna cewa, a yanzu haka ana kara samun bukatar Kajin, inda hakan ya kuma shafi rabar da Kajin a yankin Arewa.
A yanzu dai, ana sayar da ‘yan tsakin kyankyasar kwana daya akan naira 800, inda kuma ba a iya sayen ‘yan tsakin da aka kyankyashe a cikin sati biyu ganin cewa, ko wanne daya ana sayar wa akan naira 1,000 kuma babu wanda zai yarda ya sayi ko wanne daya akan naira 2,000.
Shi ma wani da ke wannan sana’a mai suna Mansur Shehu Kiru da ke da gonar Kajin da ake kira da Rahama Agro ya bayyana cewa, ya rage yawan Kajin daga 2,000 zuwa 400 saboda tsadar safarar su daga garin Ibadan zuwa Kano.
Ya ci gaba da cewa, magunguna Kajin ma sun yi tashin gwaron zabi, inda ya kara da cewa, wannan ma bababn kalubale ne da masu sana’ar ke fusktana a jihar.
Ya ce, a ‘yan tsakin na broiler a shekarar da ta wuce, ana sayar duk kwara daya ta ‘yan tsakin su akan naira 500 amma yanzu farashin ya kai daga naira 800 zuwa naira 850.
Mansur Shehu a baya ana sayar da buhun abincin ‘yan tsaki ne akan naira 3,500 , amma a yanzu farshin ya kai daga 8,000 zuwa naira 9,000.
Shi ma wani mai ruwa da tsaki a fannin Zaharaddin Yakasai wanda keda gonar kiwon da ake kira da Yaks a jihar Kano, ya sanar da cewa, abincin Kajin ya yi matukar tsada a bana, musamman saboda mastin tattalin arziki da kasar nan ke fuskanta.
Zaharaddin Yakasai ya bayyana cewa, saboda wadannan kalubalen wasu masu sana’ra sun dakatar, domin tafiyar da fannin a yanzu, akwai matukar wahala.
Ya sanar da cewa, idan ka lissafa zaka ga ba wata ribar kirki muke samu ba, inda ya ce, wasu na barin sana;ar wasu kuma sun rage yawan adadin wadanda suka kiwata wa.
A cewar Zaharaddin Yakasai, akwai matukar bukara gwamnati ta kawo mana dauki, musamman ganin yadda fannin ke taimaka wa wajen samar da ayyukan yin a kai tsaye da kuma wadanda ba ana kai tsaye ba a jihar, musamman a tsakanin matasan da ke a jihar
Zaharaddin Yakasai ya kuma koka akan yadda duk da wadanna kalubalen da masu sana’ar a fannin ke ci gaba da fuskanta, amma masu karbar haraji tin daga na kananan hukomomi har zuwa matkin jiha ba sa daga masu kafa, inda ya sanar da cewa, masu karbar harajin na karbar daga naiora 100,000 zuwa naira 300,000.
“Akwai matukar bukara gwamnati ta kawo mana dauki, musamman ganin yadda fannin ke taimaka wa wajen samar da ayyukan yi na kai tsaye da kuma wadanda ba na kai tsaye ba a jihar, musamman a tsakanin matasan da ke a jihar”.
Shi ma wani dilan ‘yan tsaki da sauran tsintsaye a jihar Abdurrahman Suleiman Tarauni ya bayyana cewa, sana’ar yanzu ba ta tafiya yadda ya kamata, inda ya kara da cewa, a yanzu ana sayar da abincin Kajin daga naira 8,000 zuwa naira 9,000, inda hakan ya sa mutane ba sa iya saye.