Sanin hali da Dabi’ar dan Adam cikin al’umma abu ne mai matukatar wahalar ganewa cikin kankanin lokaci, face an zauna da juna sannan ake iya gane hali da dabi’ar mutum.
Duk da cewa wasu na iya gane dabi’a da halayyar wasu mutanen cikin kankanin lokaci, sai dai hakan baya nufin ana iya gane halin kowa ko dabi’ar kowa a lokaci kankani. Gane macen kwarai ko namijin kwarai yayin neman aure ko fara soyayya, abu ne mai matukar wahalar gaske wajen ganewa, domin daga mazan har matan ba Tukunya bane su balle a kwankwasa.
- Matatar Man Dangote Za Ta Fara Aiki A Ranar 22 Ga Watan Mayu
- Allah Ya Yi Wa Jarumin Kannywood, Mai Mala Rasuwa
Shafin Taskira na wannan mako zai yi duba ne ga wasu batutuwa, ta fannin wasa kwakwalwa tsakanin mata da maza. Inda batun ya fara da bangaren maza wajen zabin mace guda cikin wadannan mata; 1) Mace me son kudin tsiya, irin wadda za ta iya aikata komai sabida kudi. 2) Mace me yaho wadda mijinta na saka kafa ya fita ita ma za ta saka kafa ta fita. Sai kuma bangaren Mata da su ma za su yi zabin guda cikin wadannn mazaje; 1) Namiji me mammako wanda yana da kudin amma ba zai iya fiddasu ba, kuma ba a iya cin kudinsa ko biyar. 2) Namiji me kulle irin wanda baya barin fita ko da soro ne, wanda ko me zai faru a gidansu matar ma ba zai bari ta je ba, kuma ba zai bari a shigo ba. Idan aka dauki guda cikin wadannan wacce hanya za a bi domin magance matsalar, kuma wacce shawara za a bawa masu irin wannan halin?. Mabiya shafin Taskira sun bayyana ra’ayoyinsu kamar haka;
Sunana Ibrahim Ismail Ibrahim daga Jogana Jihar Kano:
Aminci su kara tabbata ga shugabanmu Annabin tsira, kowa yayi rikoo da shi ya rabauta. A gaskiya duk cikinsu bana fata ubangiji ya bani daya daga cikin mai irin wannan halayar sabida duk mace mai masifar son kudi babu abin da ba za ta yi ba, haka mace mai yawo ma haka, amma gaskiya a alal larurati zan dau mai yawo sabida ita mai yawo daka lokacin da ka zaunar da ita ka karanta mata Allah ya ce Annabi ya ce za ta iya dainawa akasin waccan da auran naku zai iya rabuwa sabida kudin, Allah ya sa mu dace. Shawara shi ne su ji tsoran Allah, su daina hakan yana haifar da rashin samar da zaman lafiya.
Sunana Fadeelah Yakubu (Milhaat) Daga Jahar Gombe:
A gaskiya ni kam ba zan iya auren ko daya daga cikinsu ba, dalili kuwa shi ne babu yadda za a ce za a yi rayuwa haka kawai ba kudin ba, babu yadda za a ce hankalin mace zai kwanta dana Miji mai mako, Namiji mai kulle muma ni kallon mugu nake masa. Hanyar da za a magance shi kuma shi ne maza su sa tsoron Allah a zuciyar su, su sani fa amana ce aka basu wasu mazan gani suke idan aka aura musu mace to fa shikenan sai yadda suka yi da ita ba kunya ba tsoron Allah. Shawarar da zan basu shi ne su ji tsoron Allah kuma su sani idan suka ci amana to tabbas amana za ta ci su, mugun illa za su yi wa matayen nasu wanda za su sa ‘yan uwanta su rika yi mata kallon marowaciya ko kuma su dauka ba ta son zumunci ne. Kyauta na rage kiyayya tana kuma kara soyayya. Annabi (SAW) Ya ce: “An sanya ma zuciya son wanda yake kyautata mata”.
Sunana Abbas daga Jihar Gombe:
Ni a nawa ra’ayin zan dau mace Mai Yaho. Hanyar da zan bi wajen magance matsalar shi ne; zan fada mata cewa ni ba zan sake ki ba idan ta ji tsoron Allah ta daina wannan yaho mu ci gaba da zaman aurenmu, idan kuma ba ta daina ba zan kara mata kishiya ko dan kishi ma idan ta ji hakan za ta iya dainawa. Shawarar da zan bawa masu irin wanan hali shi ne; su ji tsoron Allah su daina, sabida shi aure ba wasa bane idan ba haka ba kuma za ta sa iyayenta cikin wani hali kuma zai iya kawo mutuwar auran sannan ta tonawa kanta asiri.
Sunana Princess Fatima Mazadu daga Jihar Gombe:
Wallahi gwara miji mai kulle dan da yardar Allah wata sanadi za ta zo ya barkan, In har zai bar ni jinya ban da damuwa. Hanya babba ita ce addu’a da kuma biyayya tun da ba a rage ni da komai ba. Shawara daya ce zan sashi a addu’a sannan zan ke lallabashi dan dama yawar yawo ba ta mace ba ne zaman cikin gida shi ne cikon zaman lafiya a aure.
Sunana Isma’il G. Waka daga Gwammaja Entertainment:
Na zabi Macce me son kudi, to Mace mai son kudi a ganina akwai sauki a gare ka, Dalili na shi ne; idan har Allah ya horemaka kana da kudin to za ka iya Bbya mata bukatunta, Tunda dai kudi ne matsalarta, amma mace Idan aka ce ba kudi ne damuwarta ba to idan ma ta futa baka san Inda za ta je ba, kuma baka san da wa za ta yi mu’amala ba.
Sunana Fadila Lamido daga Jihar Kaduna:
Duk ba gwara amman idan aka matsa min ya zama dole sai in dauki mai makon, domin duk bala’in mokon shi akwai yadda za ka yi da shi, ba haushe na cewa komai wayon amarya sai an sha manta, wannan magana haka take, idan ka san halin mutum sai ka ci maganin zama da shi, cikin dabara zai bayar ba tare da ya san an damu da shi ba. Shawarata ga masu mako idan zai yiwu su daina, dan bashi da wani amfani, sannu a hankali zaman zai zama na munafurci, mace za ta karbi kudinka babu lada dan ba da niyya kyautata mata ka bata ba duk da cewa kuma ta biya bukatar ta hakan ba zai taga farinka ba, ba za kuma ta daina kiranka mai mako ba, daga karshe za ka iya samun abin da macen ke iya kwakula inda sakin hannun gareka za ka yi hidimar da tafi haka ba tare da ka kashe wannan kudin ba.
Sunana Auwalu Rester Jarumi daga Gwammaja Entertainment:
Mace mai son yawo sabida ita mace Mai son yawo idan da so da kauna tsakaninta da mijinta to zai iya zaunar da ita cikin gida cikin soyayya da kauna ya fada mata illar abin da take akaitawa a cikin muslunci ya fada mata ba daidai take yi ba.
Sunana Abdul taraba daga Gwammaja Entertainment:
Ni na dauki mai son kudi dalili kuwa kudi yana da mahimmanci ga rayuwar dan Adam. Hanya daya ce zai iya shawo kan al’amarin shi ne kauna.
Sunana Khaleep saleh Tabla daga Jihar Bauchi:
Mace mai yaho dan ta fita wata kila ma ziyara ta kai wa mamarta saboda koh ta tambaye shi baya barinta kinga ai dole ta fita ko. Duk namijin da wani baya bari a shigo masa gida saboda shi ba shi da yarda ni a nawa ganin ya bata. Hanyar daya dace abi ita ce addu’. Shawarata ita ce ina kira da duk masu irin wannan halin su rinka hakuri.
Sunana Mas’ud Saleh dokadawa:
Ni gaskiya gwara me son kudin tsiya, saboda na san kudi kowa yana sonsu sai dai wani ya fi wani, kuma zan yi iya kokarina wajen bata kudin dai-dai da samuna, ko wadata ta, don na san ya fi fita yawo ko ba komai na san tana gida a zaune babu zargi tsakanina da ita. Hanyar da za a bi don magance wannan matsalar shi ne; bita mata buka tunta daidai gwargwado, sannan yawan yi mata nasiha akan rage son kudi da abin duniya, sannan kuma samar mata da sana’a don ta dogara da kanta. Shawara ita ce su gane cewa Allah ne ya dorawa mazajensu sauke duk nauyin na wajibi akansu, saboda haka indai an sauke nauyin wajibi to su godewa allah, ba sai sun tada hankula wajen karbar kudi ba, illar hakan kuma yana saka aure ya mutu saboda yawan tambayar miji kudi, ko son kudin fiye da kima. bayan haka Allah ya hana yin wannan halayen addini ya yi hani da su, don wataran sata za su yi in ba a basu ba, kuma ‘ya’ya za su koyi wannan halin daga uwarsu, su ma sun dauki hali mumuna wanda bai kamata ba.
Sunana Aminu Abdullahi daga Jihar Kano:
Mace me yaho, Yawon ta ba zai zama kullun ba kuma wani zubin sai ta tambayi mijinta kafin fitar. Hanyar magance matsalarta hana ta fita koda yaushe, kuma ka nuna mata baka son yawo matuka, kuma ka nema mata sana’ar yi a gida in sana’ar ta bunkasa zai zamana ita ma ba ta son fitar saboda kasuwancinta. Shawara ga masu irin wannan hali su sani suna abin da Allah baya so, kuma zai bada matsala a rayuwar su da iyalinsu baki daya, zai zamana basu da daraja a idon duniya, kuma za a dinga kallonsu a wulakance.
Sunana Khalifa Dan Dago daga Gwammaja Entertainment:
Gaskiya ni dai gwara na dauki mace Mai son kudi. Dalili kuwa shi ne ita da zarar za ka bata kudin to hankali zai kwanta babu tashin hankali, kuma za ku zauna lafiya. Ita kuma mace mai yawo ko me za ka bata ba za ta zauna a gida ba, ko za ka bata duniya da abin da yake cikinta ba za ta zauna a gida ba, kuma baka san inda take zuwa ba balle hankalinka ya kwanta. To a karshe dai gaskiya gwara mace mai son kudi dari bisa dari.
Sunana Abubakar Muhammad Shehu daga Jihar Kano:
Idan ni ne zan dauki ta biyun saboda wanan halin zai fi saukin magancewa a kan wancan hanyar da za a bi domun magance wanan shi ne ka sa ido akan matar ka ka hana ta fita ko nan da kofar gida idan taki sai ka fara horar da ita ko me ta tambayeka ka hanata in sha Allahu za ta gyara. Shawarata a nan ita ce shi aure ibada ne ku tsaya ku nemi Aljanar ku irin wanan halin ya kan raba aure ya sa matan su fara mu’amala da mazajen da ba muharamansu ba.