Alamu masu karfi sun bayyana a karshen makon da ya gabata cewa zababben shugaban kasa, Bola Tinubu na nuna sha’awarsa kan wanda zai zama shugaban majalisar dattawa sakamakon yadda hakan ke da matukar muhimmanci, mu-samman la’akari da rashin tabbas sakamakon koke-koke daban-daban da ke kalubalantar nasararsa a kotun sauraron rarrakin zabe.
Manyan ‘yan takarar shugaban majalisar dattawan sun hada da tsohon shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa kuma tsohon ministan harkokin Neja Delta, Sanata Godswill Akpabio da tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Mista Ad-ams Oshiomhole da babban mai tsawatarwa na majalisar dattawa, Sanata Orji Uzor Kalu da Gwamnan Jihar Ebonyi mai barin gado, Mista Dabe Umahi, na ci gaba da fafatawa a neman zaman shugabancin majalisar dattawa.
An bayyana cewa a daidai lokacin da Oshiomhole da Umahi suka dage kan cewa za su tsaya takara, akwai yunkurin yin gyaran fuska ga dokokin majalisar dattawa domin ba wa ‘yan majalisar dattijai damar tsayawa takarar manyan mukamai, saboda share wa tsohon gwamnan Jihar Edo hanya wanda ake kyautata zaton Tinubu ya fi son sa.
Wannan shi ne karo na farko da Oshiomhole da kuma Umahi za su kasance a zau-ren majalisar dattawa.
Rahotanni sun bayyana cewa jam’iyyar APC ta sadaukar da takarar shugabancin jamalisar dattawa ga yankin kudu maso kudu, yayin da yankin arewa maso yam-ma zai samar da mataimaki, dokokin majalisar dattawa sun hana fitowar sanata a karo na farko ya nemi takarar shugabancin majalisar.
A karkashin dokokin majalisar dattawa na yanzu, ba su cancanci tsayawa takara ba, saboda dadadden sanata ne kawai ya cancanci ya rike babban mukami a zau-ren majalisar.
Sai dai wata majiya mai tushe ta bayyana cewa idan har Oshiomhole ya tsaya takara, gwamnonin APC za su iya watsi da Umahi.
An bayyana cewa fargabar yiwuwar sakamakon koke-koke da aka shigar kan na-sarar da Tinubu ya samu a kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ya sanya zababben shugaban kasar da makusantansa neman dan takarar da za su amince da shi.
Wasu majiyoyi da dama sun shaida cewa bangaren Tinubu ya neman wani amintaccen abokinsa ya zama shugaban majalisar dattawa ta yadda idan har aka soke zaben shugaban kasa da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu, abokinsa zai kasance a matsayin shugaban riko na tsawon kwanaki 90.
“Akwai fargabar cewa kotun za ta iya soke zaben. Idan kotun ta soke zaben, za a bukaci shugaban majalisar dattawa ya ci gaba da rikon kwarya na tsawon kwa-naki 90,” wata majiya take shaida wa manema labarai hakan.
A halin da ake ciki kuma, kwamitin kungiyar gwamnonin APC da aka kafa ya zau-na kan batun bin tsarin karba-karba wajen raba mukaman shugabanci a majalisar dokokin kasar nan, wanda ya mika rahoto ga zababben shugaban kasa dangane da matsayin jam’iyyar APC.
Rahotannin sun bayyana cewa Tinubu ya bukaci a kafa kwamitin ne a lokacin da wasu gwamnonin suka ki amincewa da wani shiri na bai-daya da nufin karkatar da mukaman shugabannin majalisar dokokin kasar ga wasu mutane.
A cewar wata majiya, gwamnonin da ke adawa da hakan sun yi barazanar cewa za su tunkari shugabannin jam’iyyar idan har ba a bi ka’ida ba wajen zaben shugabannin majalisar tarayya.
Majiyar ta ci gaba da cewa: “Zababben shugaban kasa ya kusa kammala tsare-tsarensa na fitar da mutumin da zai shugabanci majalisar dattawa har sai da gwamnonin suka shiga tsakani suka kuma sha alwashin za su yi wa jam’iyyar aiki wajen goyon mutum na biyu a zauren majalisar a yayin kaddamar da majalisar dokokin kasar karo na 10.
“Zababben shugaban kasa wanda ba ya son ya fara gwamnatinsa da rikicin da zai iya hana shi aiki, ya bukaci kungiyar gwamnonin ta kafa wani kwamiti da zai sa-mar da tsarin da kowa zai amince da shi kan batun karba-karba wanda shugaban-nin jam’iyyar za su tattauna.”
Wata majiya da ke kusa da daya daga cikin gwamnonin, ta shaida cewa za a mika rahoton ne ranar Litinin.
Tinubu ya ki amincewa da shirin da wasu jiga-jigan sanatoci daga shiyyar Kudu maso yamma suka yi na ba shi goyon bayan ajandarsu na yin amfani da tsarin karba-karba wajen samar da shugabannin majalisa ta 10.
Wasu majiyoyi da dama sun tabbatar da cewa sanatocin da ke daukar kansu a matsayin na hannun daman Tinubu, sun yi ta aiki ba dare ba rana domin karkatar da shi kan bin tsarin karba-karba wajen zaben shugabannin majalisar dattawa na 10 ga zababbun Sanatoci biyu.
Majiyar wacce ta fito daga yankin kudu maso yamma, ta bayyana fargabar cewa matsayar da sanatocin ke yi na iya kawo cikas ga tsarin karba-karba na jam’iyyar APC a zauren majalisar a ranar da za a rantsar da sabbin shugabannin, domin akwai yiwuwar ya sake tsayawa takara karo na biyu.