• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsananin Zafin Kaye A Zaɓen Fidda Gwani Yasa Wike Sambatu – Babba Mazoji

byAbdullahi Muh'd Sheka
3 years ago
Wike

Duk zantukan da ke futa daga bakin Mai girma Gwamnan Jihar Rivers Nelson Wike sambatu ne Kawai na Zafin Kaye da yasha a Zaɓen Fidda Gwani da aka gudanar a baya. Honarabul Zaharaddeen Babba Mazoji Tsohon Dan takarar kujerar Sanata a Shekara ta 2019 Kuma guda cikin Dattijan Jam’iyyar PDP a Jihar Katsina ne ya bayyana haka ga manema Labarai a Abuja.

Honarabul Zaharaddeen Babba Mazoji yace “na saurari tattaunawar da akayi dashi inda ya bayyana wasu maganganu da basu kamata ace sun fito daga bakin mutun irin Wike ba, Wanda mutum ne mai qima a wajena kasancewar ya bayar da gagarumar  gudunmawa a baya. Abin akwai mamaki Wanda tun kafin lokacin Zaɓen fidda Gwani lokacin wani taro da akayi a Legas mun bayar da shawara inda akayi watsi da bukatar nuna wani dan Takara daga wata shiyya wanda hakan baya cikin kudin tsarin mulkin Jam’iyyar PDP.

  • Da Gaske Atiku Ya Hakura Da Wike?

“Kuma Wike mantawa ya yi sune sukayi uwa kuma sukayi makarbiya wajen tabbatar da fitowar Shugaban Jam’iyyar PDP daga arewa domin a zatonsu shikenan sai Shugaban Kasa ya fito daga kudu? Sun manta wanca kudiri ko tattaunawa da akayi a Jihar Legas cewa Kujerar Shugaban Kasa ‘yace a ruwa ta mai rabo, an aminta duk Mai sha’awa ya fito ya tallata hajarsa. Kuma ai shi Wike dashi akayi takarar fidda  Gwani na Kujerar  Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP,  mai girma Alhaji Atiku Abubakar ya rangada shi da Kasa. Sannan ko a zantawar tasa ya tabbatar da cewa mulki Allah ke bada shi ga wanda yaso, shike nan Allah ya baiwa Atiku sai ciwon hassada ya bayyana? Inji Mazoji

Da aka tambayeshi kan matsayar Wike da ‘yan barandarsa kan Ficewa daga tawagar yakin neman zaɓen Atiku, Mazoji ya bayyana cewa wannan Shure shure ne da baya hana mutuwa,  abinda Wike ya kamata ya fahimta Kashi 90%  na masu zugashi wasu mutane ne da ko a akwatinsu ba zasu iya katabus ba, wasu kuma tsoffin Gwamnoni ne data kare masu suke dan lasar abin sawa a baka daga Gwmna Wike, Wanda Ina tabbatarwa da Wike cewa sauran ‘yan Kwanaki wa’adin mulkinsa ya kare duk guduwa zasu yi su barshi. Yanzu haka wani adadi mai yawa daga cikin masu rajin goya masa baya (Wike) duk sun tabbatar da Atiku suke, Idan Kuma  sun koma kusa dashi su nuna suna tare dashi.

Da aka tambayeshi baya ganin cikin jawaban Wike ya nuna yana cikin Jam’iyyar ta PDP kuma zai ci gaba da yakarta? Babba Mazoji cewa ya yi, mu Wike ba wata barazana bace ga takarar Wazirin Adamawa, domin duniya ta fahimci Wike da ‘yan korensa Arewa ce basa kauna, kuma ya kamata na tunawa Wike idan mantawa ya yi, ya manta Shekara nawa Obasanjo ya yi akan karagar mulki, Shekara Nawa Goodluck ya yi Kuma Shekara nawa Dattijon arziki Alhaji Musa ‘Yar Adua ya yi akan mulki, duka kusan Shekara Goma Sha Huɗu’ ‘yan kudu suka yi suna mulkar mu, kuma sai yanzu da Allah ya kawo lokacin Atiku hassada zata bayyana?

LABARAI MASU NASABA

Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Da Aka Shigar Da Tinubu Kan Sanya Dokar Ta-Ɓaci A Ribas

Jam’iyyar PDP Ta Zaɓi Sabbin Shugabanni A Kwara

Babba Mazoji ya tabbatarwa da masu irin wancan ciwon hassada cewa suyi hakuri mulki Allah ke ba dashi ga wanda yaso, yanzu kuma alamu sun bayyana Wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar shi ne Shugaban kasarmu na gobe da yardar Allah. Jama’ar Nijeriya Mun sha azaba a hannun Jam’iyyar APC, ga talauci, rashin tsaro, Yajin aikin Malaman Jami’a, Sayar da kadarorin Gwamnati, Jama’a duk sun zama mahaukata saboda tsananin yunwa, wannan tasa Jama’ar  Nijeriya yanzu sun gamsu Jam’iyyar PDP itace Jirgin fiton Al’umma.

A Karshe Babba Mazoji ya yiwa Jama’ar Kasarnan busharar kyawawan manufofin Atiku Abubakar, wanda zarar Allah ya bashi wannan dama aiwatarwa kawai za’a fara, ba kamar Gwamnatin APC ba data hau mulki babu wasu kwararan munufofin ciyar da Kasa gaba. Muna sanar da Jama’a sauran kwanki kadan ya rage a kaddamar da yakin neman zabe, wanda kowa zaiga irin fitar da zamuyi domin gaisawa da al’ummar Kasa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Da Aka Shigar Da Tinubu Kan Sanya Dokar Ta-Ɓaci A Ribas
Labarai

Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Da Aka Shigar Da Tinubu Kan Sanya Dokar Ta-Ɓaci A Ribas

October 2, 2025
Jam’iyyar PDP Ta Zaɓi Sabbin Shugabanni A Kwara
Siyasa

Jam’iyyar PDP Ta Zaɓi Sabbin Shugabanni A Kwara

September 28, 2025
Tinubu Zai Gana Da Manyan Ƴan Kasuwa, Zai Ƙaddamar Da Muhimman Aiyuka A Legas
Siyasa

Tinubu Zai Gana Da Manyan Ƴan Kasuwa, Zai Ƙaddamar Da Muhimman Aiyuka A Legas

September 27, 2025
Next Post
An Nada Sanatan PDP Cikin Kwamitin Yakin Zaben Tinubu

An Nada Sanatan PDP Cikin Kwamitin Yakin Zaben Tinubu

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version