Assalamu alaikum masu karatu, barkammu da sake haduwa da ku a wannan makon wanda shi ne mako na farko a cikin Azumin Ramadan shirin namu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.
 A yau shafin na mu ya zo muku da kayatattun Girke-girke na Azumi:
- Kabilu Biyar Mafiya Tsadar Aure A Nijeriya
- Kafa Jam’iyyar Adawa: Atiku Da Wasu Sanatoci Sun Sake Sabon Yunkuri
Kamar yadda muka sani Azumi lokaci ne na girke-girke da dama, kuma lokaci da ya kamata uwargida ta tanadi kala-kalar abinci da ya kamata ta rika yi ko kuma na ce ta san mai maigida ya fi bukata lokacin buda baki da kuma lokacin sahur, sannan lokaci ne na kirkirar kala-kalar abinci don birge maigida.
 Lokacin buda baki ana so mai Azumin ya fara buda baki da Dabino saboda Sunnah ce, da shi aka ce a fara, amma ba wai dole bane. Sai kuma kayan marmari (Fruit) kamar kankana da lemo, gwanda, abarba, da dai sauransu.
Bayan wadannan ba a so mai Azumi ya fara da sanyi wato ruwan sanyi, sai ki ga wasu sun fara da ruwan sanyi to gaskiya yana kawo kullewar ciki, ana so mai Azumi ya fara da abu mai dan dumi-dumi kamar shayi ko kunu ko kuma ruwan kanwa saboda kullewar ciki ko kuma kasala da ciwon ciki don saboda mutum ya samu damar yin Sallar tarawi.
Mene ne Ruwan Kanwa?
Ruwan Kanwa wani ruwa ne da ake yiwa mai Azumi yana da dadi sosai, sannan idan mai Azumi ya sha ba ya sa kasala yana warware cikin ko hanjin cikin mutum, idan mai Azumi ya saba da shan ruwan kanwa duk ranar da bai sha ba ba zai taba jin dadi ba.
Ya ake Ruwan Kanwa?
Da farko za ki samu gero sai a surfa shi a cire masa dusa sannan a wanke shi a shanya shi ya sha iska wato ya bushe sosai, sai ki dan soya shi ya yi kamshi haka, sannan ki zuba masa kayan kamshi citta, kanunfari, musoro, sai ki bayar a nika miki shi ya yi laushi sosai kamar na kunu ki zo ki shanya shi ya bushe, daga nan sai ki ajiye shi duk idan za ki dama sai ki diba ki zuba a wani dan bokiti haka sai ki dama shi da dan ruwan Kanwa dama kin dora ruwa a wuta kamar dai yadda za ki yi kunu, idan ruwa ya tafasa sai ki kashe shi ki dan bar shi ya sha iska saboda kar ya zama kunu, sai ki zuba sannan ki zuba dan sukari haka, ki ajiye shi, haka ake shan sa da dumi.
Daga nan sai kayan soye-soye da dan dahuwar nama ki kayata dahuwar namanki ya yi kyau da dadi ya yi dan room-romo yadda ana ci ana shan romon, wani kuma yana bukatar romon ya zuba a suyar dankali ko doya shi ya sa ake so ya yi yawa romon.