Kafin daukar mataki a kan tsarin da gwamnatin tarayya mai ci ta yi na kikiro da yin amfani da kudin musayar kudaden waje a cikin kasar nan, da kasuwar musayar kudi ta kasar, ta shiga cikin halin ni ‘yasu.
Gwamnatin na da hanyoyin musayar kudade daban-daban, inda kuma a gefe daya, kamfanin jirgen sama suna da na su daban, haka suma kananan masana’antu da masana’antu na da nasu na daban da ake kira da zuba hannun jari da kuma fitar da kaya zuwa ketare wato (I&E), wanda hakan ya baiwa daidaikun mutane damar samun kudaden musayar kuadade na waje a bisa bukatarsu ta samun kudaden na musayar.
Abu mafi muni shi ne, masu bukatar samun kudaden ba sa iya samu saboda iyakance adadin da aka yi na samun kudaden na musayar.
Kazakika, wadanda ke da kudaden na musayar don su sayar da su, ba a ba su damar yin hada-hadar yin kasuwancin su a bisa ko nawa suke bukatar kan farashin da suke bukatar sayar da kudaden na musayar ba.
A baya, kudaden na musayar sun dakile masu son zuba hannun jair na keatare da na cikin gida zuba hannun jarinsu domin bunkasa tattalin arzikin Nijeriya, haka kuma akwai rashin tabbas a kan kudaden na musayar, wanda hakan ya haifar da wani babban shinge ga yin hada-hadar kasuwanci.
Bugu da kari, masu son shigowa cikin kasar don zuba hannun jari, sai suka gwammace kodai su tsaya a gefe, ku kuma su zuba hannun jarin nasu a wasu sauran kasuwannin.
Wato ma’ana, wadanda ke son samun kudaden musayar don yin wasu ayyuka, suna samun jinkiri wajen samun kudaden wanda hakan ke sanya su dakatar da bukatarsu, ta ci gaba da neman kudaden na musayar.
Hakan ya janyo tsadar da gwamnatin kasar ke samu ta kai kimanin dala miliyan 329 a duk wata a kan tallafin na kudaden musayar.
Hakan ya nuna sanar da irin illar da ake samu a kan farashin na bai daya tun daga kan masu zuba jari daga ketare da kuma masu zuba jari na cikin gida.
Sai dai, a kulla yarjejeniya a kan kayan cikin gida, hakan ya habaka kwarin guiwar masu son zuba jari a cikin Nijeriya, akwai kuma fatan da ake da shi na kara samun bunkasar zuba hannun jari a cikin tattalin arzikin kasar.
Abu mafi sauki da ake bukata shi ne yin cinikaiyyar kudaden musayar a kan farashi daya wanda hakan zai baiwa dilolin da ke yin hada-hadar kudaden na musayar yin hada-hadar ba tare da fuskantar wani shinge ba.
Bugu da kari, a bisa rahoton da bankunan hada-hadar kasuwanci na kasar suka fitar, ya nuna cewa, a cikin ‘yan watanni uku da aka gabatar da tsarin na bai daya na hada-hadar kudaden na musayar, an ruwaito cewa, bankunan kasuwanci a cikin kasar nan, a farkon zango na shekarar 2023, sun samu dimbin riba ta musayar kudaden da aka kiyasa ta kai ta Naira Tiriliyan 1.7.
Samun wannan ribar a kan kudaden musayar kudaden, an danganta hakan ne a kan karyewar farashin Naira wadda ta kai matsayin Naira 769.25 a kan dala 1 a watan Yunin 2023, inda aka kwatanta da yadda matsayin Naira yake a 2022, inda ta rufe a kan farashin Naira 461.50 , inda ya kai a kan dala 1.
Bugu da kari, kwararru a fannin hada-hadar musayar kudi, na da yakinin cewa, wannan sabon tsarin da gwamnatin mai ci ta kirkiro da shi, musamman domin a tabatar da an yi tsafatattaciyar hada-hadar musayar kudade, wanda tuni wannan tsarin a dai-daikun mutane da kuma ‘yan kasuwa suka fara ganin fa’idarsa, zai bayar da gagarumar gudunmawa wajen farfado da tattalin arzikin kasar nan .
Biyo bayan daidaita farashin kudin muyasar, masu abokan huddar da ke ajiye kudade a bankuna, wato (DMBs), suma sun yi saurin rungumar tsare-tsaren da bankunna kasuwanci suka kirkiro, musamman bisa nufin samar da sauki a wajen yin musayar kudi.
Bugu da kari, a bisa zabin sauya kudaden musaya zuwa takardar Naira, ta hanyar yanar Gizo, wannan a yanzu, ya baiwa masu huddda da bankuna damar cire kudi a bankuna ba tare da wata matsala ba haka ba  sun je kasuwar bayan fage don yin musayar kudi ba.
Wannan sauyin ya kara kwarin gwuiwa a wajen daidaita tsarin farashin na kudin musaya kari da jajircewar gwamnatin tarayya na tabbatar da ana bin diddigi da kuma gudanar da sahihiyar kasuwar ta musayar kudi.
Kazalika, tsarin ya kara baiwa bankunan kwarin guiwa wajen kirkiro da abubuwa da kuma gabatar da lalubo da mafita a kan yadda za su yi hada-hada da abokan huddarsu.
Babban misali daya shi ne, yadda tsarin ya bayar da dama sake farfado da asusun masu ajiya na bankuna da aka dakarar da su daga yin aiki, saboda masu amfani da asusun sun daina yin amfani da su, wanda kuma tsarin yaba su damar samun rance kudi da suka kai har zuwa kashi 85 a cikin dari.
Dakatar da yin amfani da Kati na hada-hadar yin hadar-hadar Niara na kasa da kasa, wannan ya baiwa bakunan damar baiwa daidaikun mutane damar yin kasuwanci daga kasa zuwa wata kasa, wanda hakan ya dakile kalubalen da ake fuskanta a hada-hadar kudaden kasa da kasa
Sanarwar dokokin hakan ya kara farashin yarjejeniyar kudin Yuro na kasar nan, inda wasu suka kara yawan farashi a cikin watanni.
Hakazalika, bayar da damar a 2033 ta karu daga kashi 2.4 zuwa kashi 78.625, wanda hakan ya zama shi ne babban karin da aka samu a cikin sama da wata biyar.
A cewar Babban Jami’a a Bolition Cap, Subomi Plumptre, kasauwar hada-hadar kudaden musayar kudin za a kara samun matukar yin gasa, musamman ganin cewa, baokan hudda za su yi sauya dala kai tsaye, ta hanyar hada-hadar yanar Gizo
Ta ce, wannna zai kara bayar da kwarin guiwa wajen samar da kirkiro da dabaru wanda kuma hakan zai bayar da dama wajen rage hada-hadar farashin kudaden musaya ga alummar gari.
Shi kuwa Baban Jami’i a Cibiyar daukaka kasuwanci mai zaman kanta wato (CPPE), Dakta Muda Yusuf, a cikin wata sanarwa da ya fitar a kwanan baya ya bayyana cewa, daga darajar ta muysar kudi, zai bayar da dama wajen zuba hannun jari da samar da ayyukan yi da zagayar kudade, inda kuma za ta kara wa masu son zuba jari kwarin guiwa.
Kazalika ya bayyana cewa, hakan zai rage cin hanci da rasahwa da dakile aikata sauran badakala da sauransu.
Bugu da kari, shi ma wani masani a fannin tattalin azrki Kelbin Emmanuel ya sanar da cewa, wannan matakin zai zai kara samar da kudaden shiga ga kamfanonin gwamnati a bisa farashin masu zuba jari da kuma masu fitar da kaya zuwa ketare.
Ya kuma yi amanna da cewa, wadanan sauye-sauyen, za su kara bunkasa tattalin arzikin kasar nan.
Sai dai, ya bayyana cewa, sauye-sauyen za su iya zuwa da kalubale, inda ya buga misalai da samun karuwar hauhawan farashin kaya da gudanar da ayyuka
Ugwu, mai fashin baki ne a kan hada-hadar kudi da ke da zama a Abuja.