Hukumar kula da lafiya ta kasar Sin NHC, ta bayyana jiya Asabar cewa, tsarin kasar na kidayar wadanda cutar COVID-19 ta yi sanadin mutuwarsu, daidai yake da na hukumar lafiya ta duniya WHO da kuma sauran kasashe.
Shugabar sashen kula da tafiyar da harkokin kiwon lafiya dake karkashin hukumar NHC, Jiao Yahui ce ta bayyana haka, yayin wani taron manema labarai, inda ta ce kasar Sin na raba mace-macen da suka jibanci cutar COVID-19 zuwa rukunoni biyu. Na farko, wadanda suka mutu sanadiyyar gazawar hanyoyin numfashi bayan kamuwa da cutar, da kuma wadanda dama can suke da matsalolin lafiya, sannan kuma suka kamu da cutar.
Ta kara da cewa, kasar Sin na sanya gazawar hanyoyin numfashi bayan kamuwa da cutar COVID cikin adadin mace-macen da cutar ta haifar.
Daga ranar 8 ga watan Disamban shekarar 2022 zuwa 12 ga watan nan na Janairu, Kasar Sin ta bayar da rahoton mutane 59,938 sun mutu sanadiyyar cutar COVID-19.
Wasu jami’ai sun bayyana yayin taron manema labaran cewa, galibin wadanda suka shiga cikin yanayi mai tsanani bayan kamuwa da cutar, da ma wadanda ta yi ajalinsu, mutane ne da suka manyata, kuma suke da wasu cututtuka na daban.
A cewar Jiao Yahui, lokacin hunturu, lokaci ne da ake samun yawaitar matsalolin numfashi, kuma yanayin sanyi kan ta’azzara cututtukan da suka shafi zuciya da kwakwalwa a tsakanin mutanen da suka manyanta.
Ta ce haduwar wadannan cututtuka da cutar COVID-19, ya kara adadin mace-mace a tsakanin mutanen da suka manyanta. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp