Manzon Allah (SAW), ya takaita cikin abincinshi da tufafinsa da wurin kwanansa a kan abin da ya zama darurar rayuwarsa (abin da dole ne da su za a rayu).
Kudi in za ka iya ajiye su a inda ya dace, ya zama alkairi amma akasin haka sai tara kudin ya zama sharri.
- Babu Sauran Burbushin ‘Yan Ta’addan Lakurawa A Arewa Maso Yamma – Ministan Tsaro
- Zarge-zargen Shugaban Sojin Nijar Kan Nijeriya Ba Su Da Tushe – Gwamnatin Tarayya
Manzon Allah (SAW) ya kasance mai tsantsaeni, bai dauwara wa rayursa cewa sai tufafi iri kaza zai sanya a jikinsa ba, duk irin wanda ya samu, shi yake amfani da shi.
A zamanin rayuwar Annabi (SAW), ya kasance yana sanya abaya (duk rigar da take da tsagi a gaba, tun daga wuya har kasa) da zani, sabida ba al’adar larabawa ba ce sanya wando, wata rana Annabi (SAW) ya je kasuwar bani Kainuka’a ya ga wando, sai ya ce wannan zai yi wa mata kyau, sabida ya fi suturce su a kan zani, ba laifi ne mace ta sanya wando ba sannan ta sa zani daga baya, sabida yanzun wando ya zama na maza duk da cewa, yanzun akwai nau’in wando irin na mata. Amma al’adar Larabawa, zani suke sawa, har yanzun mutanen Yamen, zani suke sawa. Manzon Allah (SAW) yana sa tufafi mai kauri mara santsi.
Amma duk da haka, Annabi (SAW) yakan raba wa Sahabbai da bakinsa alkyabba ta afarma mai hula a baya, wata rana kuma ya raba alkyabba ta dibaje mai alhariri shi kuma ya dauki wacce ko kwalliya ba ta da shi. Yana rarraba kayayyakin da aka kawo masa na ganima ga wadanda suke kusa da shi da wadanda suke nesa da shi.
Manzon Allah (SAW) ya hana maza sanya kayan alhariri, wata rana wani sarki ya aiko masa da alkyabba ta alhariri duk an mata kwalliya da zinari, sai Annabi (SAW) ya ce, wannan irin kayan wanda bai da rabo a lahira ne. sai Annabi (SAW) ya ce akai wa Sayyadina Umar, dan aike na zuwa ya mika wa Sayyadina Umar, sai ya amsa ya yo wurin Annabi (SAW) yana kuka, ya ce ya Rasulallahi ka ce irin wannan riga, ta wanda bai da rabo a lahira ne, Annabi ya yi murmushi ya ce, Ya Umar! Ba kai nace ka sa ba, dan’uwanka da ke Kafirci nake so ka ba wa. Malamai, sabida wannan suka yi fatawa cewa, in kana da aboki wanda ba Musulmi ba, za ka iya ba shi kyautar abin da Musulunci ya haramta, yanzun ba kai ka yi amfani da shi ba ake nufi.
Alfahari da kayan sawa, ba su cikin dabi’un girma da daukaka, wannan sunnar mata ce, ado da kayan sawa sabida maigida ya gani ya ce ya yi kyau ba namiji ba.
Ma’anar wannan shi ne, kar Mutum ya ga cewa, da kayan sawa yake samun daraja, kar ka yi wa wanda bai da shi alfahari, kar ka ki neman Ilimi sabida alfahari da tufafi, wannan ake nufi. Amma lallai, kaya suna daga cikin abubuwan da suke tsare mutunci.
Shehu Sukairija ya ce wa Shehu Ibrahim Inyas “kar ka kara sanya kaya marasa kyau, na hore ka da sanya kaya masu kyau, duk wanda zai kalle ka, kayan jikinka kawai yake fara kallo”, Shehu Sukairija ya rasu tun wuraren 1953 amma tun a wannan zamani dabi’ar mutane ta canza. Amma alhamdu lillah… duk wanda ya ga hotunan Shehu na farko zai ga hakan amma daga baya hotunan Shehu sun sauya da kayan alfarma. Abin nufi a nan, kar mutum ya ga cewan, kayan ne ya ba shi daraja sai dai kawai al’ada.
An ruwaito cikin wani Hadisi, Annabi (SAW), ya sanya wasu kaya, idan za a kiyasta kudinsu, za su yi kayan rakumi Tara (9). Lallai wannan kaya ne masu tsada da alfarma.
Don haka, kowa ya sanya tufafi masu kyau amma kar ya ga darajarsa kadai a cikin tufafin.
Abul Hasanil Shazali, shi ya fara wa Sufaye fada kan su fara sanya tufafi masu kyau, sabida al’adar Sufaye, sanya tufafi marasa kyau. Ya sha wuya sosai kan kokarin sauya tunanin sufaye kan fara amfani da tufafi masu kyau.
Shehu Tijjani Abul Abas, ya kasance yana horar almajiransa da su dinga yi wa kayansu Bula (Ma’ana su dinga sabunta tufafinsu).
Amru bin Hisham ya ruwaito hadisi daga Mahaifinsa, ya ce, Annabi (SAW) ya ce, “Innallaha yuhibbu an yara asra ni’imatihi ala abdihi” cewa, lallai Allah yana so ya ga gurbin ni’imarsa a jikin bawansa. In Allah ya yi maka ni’ima, yana so ya gan ta a tare da ita, wannan ita ce godiyar ni’ima, amma Allah ya yi maka ni’imah ka boye, kamar ka nuna wa Ubangiji cewa ba ka son Ni’imar ne, kana ce masa bai yi maka komai ba ko kuma nau’i ne na rowa.
Ba laifi ba ne face alamun girma ne mutum ya yi sana’a ko aiki ya samu kudi ya sa tufafi mai kyau. Wata rana Annabi (SAW) ya yi wa’azi mai zafi ya zargi girman kai, sai wani sahabi ya tashi ya ce, ya Rasulallahi, Allah ya yi ni Mutum ne mai son ganin rawanina ya fi na kowa kyau da alkyabbata ta fi ta kowa kyau da takalmina ya fi na kowa kyau, sai Annabi (SAW) ya ce masa wannan ba shine girman kai ba, girman kai shi ne kin gaskiya da danne hakkin mutane. Amma halal dinka, duk tufafin da kasa mai kyau ba laifi.
Abin da ake yabo a tufafi shi ne tsaftarsu, kazanta ba ta da mahalli a addini.
Sai dai, ana son mutum ya dinga sanya tufafi tsaka-tsaki, in kai ba sarki ba ne, kar ka yi shiga irin ta sarakai, an so ka yi tsaka-tsaki, kai ba babban Alhaji ba, kar ka yi ta Asusu don ka sayi kaya irin na Babban Alhaji. Duk abin da ya zama a al’ada mutum mai wani girma ko wata daraja bai dace ya aikata ba ko ya sanya a jikinshi, to kar ka aikata hakan misali (A al’adar kabilar Hausa, Malami ba za a ganshi da gajeren wando ba). Shari’a ta zargi kaiwa kololuwa ko zama na karshe a kan sanya tufafi.
Wanda Allah ya ba shi rufin asiri ya gode wa Allah ta hanyar amfani da abin da Allah Ya rufa masa asiri da shi, wannan zamani, ma’aunin bin Allah a wurin ‘yan duniya shi ne su ga duniya a tare da kai, don haka duk wanda Allah ya bai wa ni’imah ya gode masa ya yi amfani da ita ta hanyar yadda ya dace ba don neman girma a cikin ni’imar ba. Ya Allah ka ba mu ni’imarka a hannunmu ba a zuciyarmu ba! Aminn.
An karbo Hadisi daga Sa’adu bin Abi Wakkas ya ce, Annabi (SAW) ya fada cewa “Arba’un minas sa’adati: Almar’atus salihatu wal marhalul wasi’u wal jarussalihu wal markabul hamiru” Abu guda Hudu (4) suna daga cikin arziki: Mace mai halin kirki ba na tsiya ba, da gida mayalwaci, da makwabci nagari mai halin kirki, da abin hawa mai sanya hutu ba mai rikici ba.
“Arba’un minash shaka’i: “Almar’atus su’i wal jarussu’i wal markabus su’i wal maskanud dayyiku” Abu guda hudu (4) suna daga cikin tsiya: Mace mai halin banza, da makwabci mai halin banza kuma mai wuyar hali, da abin hawa mai wahalarwa, da gida kuntatacce. Ibn hibban ya ruwaito a cikin sahihansa.
Amma wanda aka tattaro masa kan arzikin kasa da ababen hawa da dukiyoyi amma hakan ba ta sa shi girman kai ba, ya koma ya yi kankan ga Allah, wannan dukiyarsa ba za ta cutar da shi ba. Hasali ma, lokutan da ya sa sabbin kaya, lokutan ya fi kankan da kai ga Allah. Ya tara falalar gudun duniya da ta arziki.