Wannan tsari shi Bature ya kira da ‘calendar method’ ko ‘calendar period’ wanda akan kaurace wa saduwa a wasu kebantattun kwanaki a yayin da ake neman kauce wa shigar juna biyu saboda wasu dalilai. Bayanan da za su biyo baya sun kunshi:
– Abunda ke jawo ciwon ciki ko ciwon mara ga mafi yawan mata yayin da suke haila da kuma wasu kwanaki can bayan Haila.
– Yadda ma’aurata za su yi ‘family planning’ ba tare da shan magani ko saka ‘Implanon’ ba.
– Abin da ke fito wa wasu mata mai kamar majina bayan wasu kwanaki da gama haila
Zanyi amfani da kalmomin Hausa kamar ko yaushe domin samun saukin fahimta, su kuma kalmomin turancin da ban san ma’anarsu da Hausa ba zan yi kwatancen da za a gane.
Wannan hanya ta ‘family planning’ abin da bincike ya tabbatar shi ne tana da sahihanci na kaso 88 — 95% cikin dari na hana shigar ciki.
Toh sai dai duk da haka Allah yakan iya canja ikonsa ko da anyi hakan kuma a samu haihuwa, Amma Insha Allah ba a cika samun ciki ya shiga ba idan aka kiyaye hakan.
A jikin mahaifar mace, (Uterus) idan kuka lura, za ku ga wasu abubuwa kamar hannu guda biyu, daya gefen dama dayan kuma gefen hagun wato bututun da ake cewa (FOLLOPIAN TUBE) a turance wanda ta ciki a rarike yake kamar ‘pipe’ din ruwa… to a can karshe a bakin kowanne fallopian akwai wani kwanson abu kullutu (Obary) wanda a cikinsa ne akwai wasu kwayaye.
Duk sanda Mace tayi haila bayan Jinin ya dauke da kwanaki 14, wancan abu da muka ambata da Kullutu yana sakin wadancan koyayen, wadanda su ne sinadarin da ake hadawa a samu da wato juna biyu.
Wadannan kwayaye idan aka sake su sukan biyo bututun su shigo cikin mahaifar mace su yi kwanaki 2 wato awanni 48’ daga nan idan babu abin da ya zo ya taba su wato na daga maniyin namiji (sperm) to za su mutu.
Toh sai dai kafin a saki wadannan kwayayen su tafi mahaifa jiran maniyyin domin samar da ciki, akwai abin da Allah ya halitta a cikin mahaifar mace wanda kan zo ya share mahaifarta sosai (estrogen), domin mahaifar za ta yi bako, wanda bakon kuwa shine wannan Kwan.
Akwai wasu jijiyoyi guda biyu na jini, a gefen dama da hagu na mahaifar mace, idan aka zo aka share mahaifar to wadannan jijiyoyin za su cika da jini sosai, sai su koma ja-ja-wur, suna jiran wannan bakon da zai shigo mahaifa saboda su yi amfani da wannan jinin da suka cika kansu da shi su ba wa bakon a matsayin abinci na tsawon awanni 48 da Kwan kan iya rayuwa.
Wanda in kwan ya zarce haka ba tare da maniyyi ya zo ya same sa ba toh lalacewa zai ya mutu.
Shi kuwa Maniyyin namiji yana yin kwanaki 3 wato awanni 72 a cikin mahaifar mace kafin ya mutu, sabanin na mace da ke kwana 2 (48hrs).
Idan mun fahimci wadancan bayanan da suka gabata, to yanzu sai mu hada su waje daya muga yadda abin yake.
Idan Mace ta gama haila da kwanaki 14 to wancan abun mai kamar tiyo wato bututun (follopian tube) da ya hace kwanson OVARY zuwa cikin Mahaifa (UTERUS) wadannan kwayayen da ke cikin OBARY ta cikinsa suke shigowa cikin mahaifarta su jira maniyyin namiji ya zo ya same su wanda ake kira (OVULATION).
Idan sanda suka shigo Mahaifa aka yi dace Namiji ya sadu da mace dama ya zuba mata maniyyi ko da kuwa kwanaki 2 da suka wuce ne akwai saduwar to komi kankantar Maniyyin nan ya wadatar da su, Maniyyin zai zamo musu kamar taki don haka za su baibaye sa su hadu su yi ta girma babu zancen mutuwa kuma wanda da haka ne kuma Allah zai ta sarrafa shi har ya maida shi jariri ya zamo mutum.
To idan kuwa sanda kwan ya shigo cikin Mahaifa babu wani Maniyyi da ya shigo gurin a dalilin rashin saduwa da macen da ba a yi ba to wadannan kwayayen za su mutu bayan sun yi awa 48 (kwanaki 2) kamar yadda na fada muku a baya cewa kwan mace bai wuce kwana 2 zai mutu in bai hadu da maniyyi ba.
Toh idan kuma suka mutu to za su biyo cikin al’aurar mace sai su fito, shi ne sai ka ji mata na tambayar sukan ga wani abu mai kamar majina-majina yana fito musu a al’aura ta wani lokaci, wanda wannan shi ne abin da ke fitowar ba wai ‘infection’ ba ne. Kuma in ‘yan mata ne da za ku lissafa za ku ga sanda yake fitowar akalla lokacin kun yi ko kun kusa sati 2 da gama haila.
Wannan ya sa malamanmu a musulunci ke cewa babu komai a kan wannan abun idan mata sun gani kawai ta wanke shi ba shi da wani hukunci, ba wanka ake ba. Amma in dai ba sau 1 a wata take ganin wannan ba kuma ya zamto ba irin wajen sati 2 ne da gama haila ba toh kila abin da kike fitarwa wannan yana da alaka da ‘INFECTION’ musamman idan dususu yake ko kuma kika ji ma yana karni.
Duk hakan ya faru ne adalilin rashin shigar Maniyyi da zai girmar da wancan Kwan, tun da kun ga budurwa dama ba aure gare ta ba.
Daga Shafin Tattaunawar Kiwon Lafiya na Dr. Aisha