Tawagar gwamnatin Nijeriya ƙarƙashin jagorancin mai ba da shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ta gana da Shugaban Chadi, Mahamat Idriss Déby Itno, a yau Lahadi.
Wannan ya biyo bayan ficewar gwamnatin Chadi daga Multinational Joint Task Force (MNJTF), wata haɗakar ƙungiyoyin Sojojin ta yankin da aka kafa domin yakar ta’addanci a yankin tafkin Chadi.
- Hasashe A Kan Sabon Yunkurin el-Rufai Da Zargin Ficewarsa APC
- Sojojin Chadi Sun Fatattaki ‘Yan Boko Haram Zuwa Kamaru Da Nijar Da Nijeriya
Tawagar ta ƙunshi babban Hafsan Sojojin Najeriya, Janar Christopher Musa, Shugaban Sashen Leken Asiri na Tsaro, Manjo Janar Emmanuel Undiandeye, da Kwamandan MNJTF, Manjo Janar Ali Salau, tare da wasu manyan jami’an tsaro. Tawagar ta miƙa sako daga Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ga Shugaba Déby.
A cikin sakon, Shugaba Tinubu ya isar da ta’aziyyarsa tare da nuna goyon baya ga Chadi sakamakon harin ta’addanci da aka kai a tsibirin Barkaram, wanda ya yi sanadin mutuwar Sojojin Chadi da dama. Ganawar ta kuma ƙara jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin Nijeriya da Chadi wajen magance ƙalubalen tsaro da yaƙar ta’addanci.
Dukkan ƙasashen sun jaddada ƙudirinsu na ƙafafa haɗin kai domin inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin tafkin Chadi. Wannan hadin gwuiwa na nufin daƙile barazanar ta’addanci da kawo ci gaba a yankin.