Gwamnatin jihar Kano ta sanar da karin kwanaki 60 domin sabunta takardun shaidar mallakar fili a jihar (CofO).
Gwamnatin jihar ta kuma yi gargadin cewa, masu takardar mallakar filaye da suka ki bin wannan sabon wa’adin, za su iya rasa filayensu, duba da ka’idojin mallakar filaye da ake da su a jihar.
- Hafsan Soji Ya Gana Da Shugabanni A Filato Kan Hare-haren Da Suka Yi Ajalin Mutane
- Kyautar LEADERSHIP Ta Kara Zaburar Da Mu Kan Sauke Nauyin Al’ummar Jigawa Akanmu – Gwamna Namadi
Kwamishinan tsara birane, Abduljabbar Mohammed Umar ne ya sanar da hakan yayin ganawa da manema labarai ranar Talata a hedikwatar ma’aikatar da ke Kano.
Ya ce karin wa’adin na baya-bayan nan ya biyo bayan cikar wa’adin farko na ranar 1 ga Afrilu, 2025, wanda aka sanya tun da farko a ranar 24 ga watan Janairu.
Umar ya kara da cewa, duk da wannan karin wa’adin, amma an ci gaba da samun karancin fitowar masu filaye domin sabunta takardunsu.
Domin tabbatar da bin ka’ida, kwamishinan ya yi gargadin cewa, nan ba da jimawa ba, za a buga sunayen wadanda ba su bi ka’ida ba a jaridun kasar nan da kuma nuna su a allunan sanarwa a muhimman wuraren gwamnati da suka hada da dakin karatu na jihar Kano, Sakatariyar Audu Bako, Gidan Murtala, da kuma babbar kotun jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp