Tsohon ɗan takarar gwamna a jihar Legas na jam’iyyar PDP, Dr. Olajide Adediran, wanda aka fi sani da Jandor, ya sanar da koma wa jam’iyyar APC mai mulki. Wannan sanarwar ta zo ne bayan kwanaki biyu kacal da ya fice daga jam’iyyar PDP.
Jandor ya ba da sanarwar koma wa jam’iyyar APC ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a ofishin yaƙin neman zaɓensa da ke Ikeja a ranar Litinin. Ya bayyana cewa ya yi shawarwari da shugaban ƙasa Bola Tinubu, tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, da wasu manyan mutane a fagen siyasa bayan ya fice daga PDP.
- El-Rufai Ya Yi Alƙawarin Haɗa Abokan Hamayya Don Yaƙar APC A Zaɓen 2027
- Ban Bar PDP Ba, Ina Gangamin Hadin Gwiwa Ne Don Tunkarar APC A 2027 – Atiku
Kakakin Jandor, Gbenga Ogunleye, ya tabbatar da cewa taron da ya yi da shugaban ƙasa ya gudana ne a ranar Litinin da ya gabata. Ya kuma bayyana cewa Jandor ya gana da wasu manyan shugabanni kamar tsohon shugaban ƙasa Ibrahim Babangida, tsohon shugaban mulkin soja Abdusalami Abubakar, da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar SDP a zaben 2023, Prince Adewole Adebayo, domin yin shawarwari kan matakin da ya ɗauka.
Haka kuma, sakataren jam’iyyar PDP na ƙasa da wasu shugabannin jam’iyyar sun ziyarce shi kwanan nan domin roƙonsa ya dakata kan matakin ficewa daga jam’iyyar. Duk da haka, Jandor ya ƙuduri aniyar ci gaba da shirye-shiryensa na siyasa a cikin jam’iyyar APC.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp