Dan takara a jam’iyyar NNPP a zaben gwamnan jihar Ondo da aka yi a ranar 16 ga Nuwamba, 2024, Hon. Olugbenga Edema ya fice daga jam’iyyar.
Edema wanda ya mika takardar murabus dinsa ga shugaban jam’iyyar NNPP na yankin Mahin (Ward 11) ta karamar hukumar Ilaje a ranar Lahadi, ya bayyana jam’iyyar a matsayin wacce ba ta shirya ba sam.
Edema ya sha kaye ne a zaben da gwamna mai ci Hon. Lucky Aiyedatiwa ya yi nasara a zaben gwamnan jihar a ranar 16 ga Nuwamba, 2024.
Sai dai a cikin takardar murabus din, Edema ya bayyana rashin tsarin jam’iyyar a matsayin dalilin da ya sa ya fice daga jam’iyyar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp