• English
  • Business News
Tuesday, November 4, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsohon Daraktan Yakin Neman Zaben Tsohon Gwamnan Bauchi Ya Koma Labour Party

by Khalid Idris Doya
3 years ago
Bauchi

Tsohon daraktan yakin zaben tsohon gwamnan jihar Bauchi, Muhammadu Abdullahi Abubakar, wato Alhaji Garba Sarki Akuyam, ya shelanta ficewa daga jam’iyyar APC tare komawa cikin jam’iyyar Labour Pary (LP) tare da daruruwan magoya bayansa.

Akuyam wanda tsohon kwamishinan kudi da ci gaban tatttalin arziki na jihar Bauchi ne, ya shelanta komawa LP ne a ziyarar da ya kai wa shugaban jam’iyyar a jihar Bauchi, Barista Hussaini Saraki a ofishin jam’iyyar jiya, yana mai cewa, ya tuntubi masu ruwa da tsaki da magoya bayansa kafin daukan wannan matakin.

  • ‘Yan Jihar Bauchi Sun Yabawa Buhari Kan Amincewa Da Ci Gaba Da Amfani Da Tsohuwar 200
  • Dan Takarar Gwamnan ZLP A Bauchi Ya Musanta Janye Takararsa

Akuyam ya bayyana cewar dalilansa na ficewa daga cikin APC sun hada har da rashin gamsuwarsa da yadda ake gudanar da lamura a cikin jam’iyyar a matakin jiha da ma kasa, kana ya bibiyi tarihin Peter Obi da irin nasarorin da ya cimma a rayuwarsa, don haka yana da kwarin guiwar Peter zai iya shawo kan matsalolin da suke addabar kasar nan.

Ya kara da cewa a matsayinsa na wanda ya ke da gogewa a bangaren siyasa da jagoranci a jam’iyyar APC har ta kai ga samun nasara a zaben 2015 da ya gudana a jihar Bauchi, bai gamsu da yadda ake tafiyar da lamura a cikin jam’iyyar ba a halin yanzu, don haka shi da daruruwan magoya bayansa suka fice daga cikin jam’iyyar.

Ya kuma kara da cewa, abokin takarar Peter, Yusuf Datti Baba Ahmed, ya fito daga fitacciyar zuri’a a arewa kuma yana da kyakkyawar alaka da su, don haka ya ga dacewar ya koma cikin jam’iyyar LP domin bada tashi gudunmawar wajen ganin sun samu nasarar lashe zabukan da ke tafe.

LABARAI MASU NASABA

Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha

“Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump

Garba Sarki Akuyam tsohon kwamishinan bunkasa yankunan karkara na jihar Bauchi ne, ya bada tabbacin cewa zai yi dukkanin mai yiyuwa domin ganin nasarar jam’iyyar a dukkanin matakai, ya kuma nemi alfarmar jagororin jam’iyyar da su amince da shi hannu biyu-biyu.

A jawabinsa na maraba, shugaban jam’iyyar Labour Party a jihar Bauchi, Barista Hussaini Saraki, ya shaida cewar wannan babban nasara ce a garesu kuma yana mai bai wa Akuyam da sauran magoya bayansa tabbacin samun adalci a jam’iyyar.

“Tabbas samun kwararren masanin siyasa kuma masanin tattalin arziki a cikin jam’iyyarmu babban nasara ce a garemu. Sannan, yadda jama’a suke tururuwar shigowa cikin LP a jihar Bauchi na nuna mana irin gagarumar nasarar da za mu iya samu a zaben da ke tafe.”

Ya kuma nuna kwarin guiwarsa na samun nasarar jam’iyyar a dukkanin matakai, yana mai kira ga sauran jama’a da su shigo a dama da su domin ceto kasar nan daga halin da take ciki.

Saraki daga bisani ya jinjina wa Sarkin Akuyam bisa daukar wannan matakin fi dacewa domin hada karfi da karfe wajen ceto Nijeriya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha
Siyasa

Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha

November 4, 2025
“Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump
Labarai

“Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump

November 3, 2025
Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna
Manyan Labarai

Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna

November 1, 2025
Next Post
An Bude Baje Kolin Fina-finai Kan Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya”

An Bude Baje Kolin Fina-finai Kan Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya”

LABARAI MASU NASABA

China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya

China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya

November 4, 2025
2023: Me Ya Sa Ake Rububin Wike?

Atiku Ya Fice Daga PDP Saboda Na Ƙi Bari Ya Lalata Mana Jam’iyya – Wike

November 4, 2025
Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha

Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha

November 4, 2025
Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi 

Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi 

November 4, 2025
Jami’an Tsaro Sun Dawo Da Fasfo Ɗin Sanata Natasha Bayan Ƙwace Shi A Abuja

Natasha Ta Zargi Akpabio Da Sanya Jami’an Tsaro Su Ƙwace Mata Fasfo A Filin Jirgin Saman Abuja 

November 4, 2025
Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo

Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo

November 4, 2025
Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump 

Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump 

November 4, 2025
Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

November 3, 2025
Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

November 3, 2025
An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

November 3, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.