Tsohon firaministan kasar Japan Yoshihiko Noda, ya soki kalamai marasa dacewa da firaministar Japan mai ci Sanae Takaichi ta furta dangane da yankin Taiwan na Sin, yana mai bayyana kalaman nata a matsayin na wuce gona da iri, kuma masu matukar hadari.
Noda, wanda a yanzu haka ke jagorantar jami’iyyar adawa ta CDPJ, ya yi tsokacin ne a jiya Lahadi a gundumar Nagasaki, inda ya ce, Takaichi ta zarce iyaka, kuma alakar Japan da Sin ta shiga yanayi na dar-dar, kamar dai yadda kafar watsa labarai ta Kyodo ta ruwaito.
A wani ci gaban kuma, kafar gidan talabijin ta Fuji dake Japan ta zanta da shugaban sashen tsara manufofin jam’iyyar adawa ta CDPJ Satoshi Honjo, wanda a cikin tsokacinsa ya ce, kalaman da Takaichi ta furta sun nuna rashin fahimtarta ga dokokin tsaro, da karancin saninta game da matsayin yankin Taiwan ga babban yankin kasar Sin.
A ranar 7 ga watan nan, yayin da take jawabi a majalisar dokokin kasarta, firaminista Takaichi ta bayyana cewa, matakin babban yankin kasar Sin na amfani da jiragen ruwan yaki, da karfin soji kan yankin Taiwan na iya zama barazana ga dorewar Japan. Ta kuma kara da cewa, bisa tanadin dokokin kasarta, dakarun kare kasa na Japan na iya aiwatar da matakan kariya na bai daya, idan har aka lura matakin na Sin na iya zama mai hadari ga dorewar Japan.
Duk da suka daga bangarori daban daban, Takaichi ta nace cewa kalaman nata sun dace da dadaddiyar matsayar gwamnatin Japan, kuma ba ta da niyyar janye su.
Ma’aikatar raya al’adu da yawon bude ido ta kasar Sin ta fitar da sanarwa a jiya Lahadi, wadda ke kira ga al’ummunta da su yi taka-tsantsan a kwanakin nan wajen zuwa yawon bude ido kasar Japan.
Game da hakan, masani a kwalejin bincike ta Nomura Takahide Kiuchi, ya bayyana a jiyan cewa, raguwar yawan Sinawa masu zuwa yawon bude ido Japan, zai haifar da raguwar GDPn kasar ta Japan da kashi 0.36%, kana hasashen yawan asarar tattalin arziki da hakan zai haifar zai kai JYE tiriliyan 2.2, kwatankwachin kudin Sin yuan biliyan 101.6.
Bayanai sun nuna cewa, kasar Sin ce babbar abokiyar ciniki mafi girma ta Japan, kasa ta biyu mafi girma wajen fitar da kayayyaki zuwa kasar, kana babban tushen shigar da kayayyaki zuwa kasar. A shekarar 2024, jimillar darajar ciniki tsakanin Sin da Japan ta kai dalar Amurka biliyan 308.3, inda yawan kudin da Sin ta kashe wajen shigo da kayayyaki daga Japan ya kai dalar Amurka biliyan 156.25.
Kididdigar hukuma mai kula da yawon bude ido ta Japan, ta nuna cewa jimillar kudin da masu yawon bude ido na Sin suka kashe a Japan a shekarar 2024 ya haura na al’ummun sauran kasashen duniya.
Manyan ’yan siyasa, da masana masu fashin baki, da kafafen watsa labarai na yankin Taiwan, sun yi Allah wadai da kalaman tayar da husuma na firaministar Japan Sanae Takaichi dangane da yankin Taiwan na Sin, suna masu bayyana kalaman nata a matsayin wadanda suka illata moriyar al’ummun Taiwan, wato mazauna yankin dake fatan wanzuwar zaman lafiya da daidaito a daukacin mashigin Taiwan.
Da yake tsokaci kan hakan, tsohon shugaban jam’iyyar Kuomintang a yankin Taiwan Ma Ying-jeou, ya ce batutuwan da suka shafi bangarori biyu na mashigin Taiwan ba sa bukatar tsoma bakin sassan waje, yana mai jaddada cewa al’ummunsu ne kadai ke da alhakin warware su. Jami’in ya kara da cewa, Sinawa na bangarorin mashigin Taiwan biyu na da basira, da ikon warware sabaninsu cikin lumana.
Shi ma a nasa tsokaci, mawallafin mujallar “Observer” Chi Hsing, cewa ya yi, a yayin mamayar dakarun Japan, al’ummun Taiwan ba su taba dakatar da nuna turjiyarsu ba. Don haka duk wani mai kaunar adalci dake Taiwan zai yi tir da kalaman na firaminista Takaichi.
Hsieh Chih-chuan, mai fashin baki kan batutuwan siyasar Taiwan, ya ce kalaman na Takaichi sun sabawa ainihin tarihi da dokokin kasa da kasa. Daga nan sai ya gargadi ’yan aware masu rajin neman ’yancin kan Taiwan, da kada su yaudari kansu bisa kalaman na Takaichi. Domin kuwa ba makawa Sin za ta kasance kasa daya dunkulalliya.(Saminu Alhassan、Amina Xu)













