Tsohon Gwamnan jihar Kwara a zamanin Mulkin soja, Group Captain Salaudeen Latinwo (mai ritaya), ya rasu.Â
Offa-born Latinwo ya zama Gwamnan tsohowar jihar Kwara ne a tsakanin alif 1983 zuwa 1985.
- Yadda ‘Hackers’ Ke Amfani Da Hanyar Smishing Wajen Yin Kutse
- Asalin Abin Da Ya Sa Barayi Suka Kashe Sheikh Albani Kuri
Latinwo ya na daga cikin manyan jami’an sojan sama (NAF)da aka dauka na farko-farko a shekarar 1963 da ya taka rawa sosai wajen cigaban jihar da kasar nan.
A sakonsa na alhini da ya fitar a ranar Asabar, Gwamnan Kwara, Abdulrahman AbdulRazaq, ya mika ta’aziyyarsa ga al’ummar jihar, musamman al’ummar yankin Offa bisa rasuwar Latinwo.
AbdulRazaq, a sanarwar da babban sakataren watsa labaransa, Rafiu Ajakaye, ya fitar, ya misalta rasuwar Latinwo a matsayin babban rashi ga illahirin jihar bisa kasancewarsa dattijo mai kishin kasa da ke da gogewa da kwarewa marar misaltuwa.
“A madadin AbdulRazaqs, gwammati da al’ummar jihar Kwara, gwamna ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan marigayi tsohon Gwamnan a zamanin mulkin soja, al’ummar Offa da sojoji bisa wannan babban rashin,” a cewar sanarwar daga fadar gwamnatin jihar.
Kan hakan, Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya jikansa mamacin ya sanya shi cikin Aljanna, ka na ya yi fatan Allah zai bai wa iyalan mamacin da wadanda ya rasu ya barsu hakurin juriyar rashi.
Kazalika, shi ma a sakon jajentawarsa, Sarkin Illorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya misalta rasuwar Latinwo a matsayin babban rashi da jihar da kasar Nijeriya suka yi.
Sulu-Gambari, a wata sanarwar da kakakinsa, Abdulaziz Arowona ya sanya wa hannu, ya kuma misalta Latinwo a matsayin jajirtacce kuma hazikin sojan saman da ya mulki jihar Kwara yadda ya dacewa.
Sarkin ya kuma ce marigayin ya kasance mutum mai yaki da rashin da’a da rashawa, wanda ya zama madubi a Mulkin Buhari/Idiagbon zamanin Mulkin soja a Nijeriya.
Sai ya yi addu’ar Allah jikan mamacin ya albarci bayansa.