Tsohon gwamnan Jihar Neja, Mu’azu Babangida Aliyu, ya bukaci a yi wa duk wanda ya kashe jami’in tsaro hukuncin kisa.
Ya ce wannan mataki zai karfafa gwiwar jami’an tsaro tare da kare su, wanda zai kara musu kishin kasa.
- Guguwa Mai Ƙarfi Ta Sa An Soke Wasan Liverpool Da Everton Na Yau
- Shekarar 2024 Babban Kalubale Ne Ga Ma’aikatan Nijeriya – Kungiyar NLC
Aliyu ya yi wannan bayani ne yayin bikin yaye daliban kwas din Executive Intelligence Management Course (EIMC 17) a makarantar National Institute of Security Studies (NISS) da ke Abuja.
Ya yi tir da kashe sojoji sama da 30 a Jihar Neja a shekarar 2023, inda ya caccakar rashin daukar mataki mai karfi a kan lamarin.
Mai bayar da shawara kan harkokin tsaro na kasa, Nuhu Ribadu, wanda ya wakilci Shugaba Bola Tinubu, ya jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da tabbatar da zaman lafiya tare da gurfanar da masu aikata laifi a gaban shari’a.
Kazalika, Daraktan DSS, Adeola Ajayi, ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa hukumomin tsaro suna aiki don tabbatar da tsaro a fadin kasar nan.
Bikin ya yaye dalibai 91, ciki har da jami’an tsaro daga kasashe biyar: Chadi, Gambiya, Ghana, Côte d’Ivoire, da Rwanda.
Manyan baki kamar Ministan Birnin Tarayya, Nyesom Wike; Ministan Kudi, Wale Edun; da Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, sun halarci taron.