Tsohon Kwamishinan Kudi na jihar Sakkwato, Hon. Abdussamad Dasuki ya bayyana cewar, babu kamshin gaskiya ko kadan kan ikirarin sayar da hannun jarin naira biliyan 16 a lokacin gwamnatin Tambuwal kamar yadda ya bayyana a yayin bayar da shaida a gaban hukumar binciken ayyukan tsohuwar gwamnatin jihar daga 2015- 2023.
Dasuki, wanda a yanzu ke wakiltar Kebbe/Tambuwal a majalisar wakilai ta tarayya, ya bayyana cewar ba ya da masaniyar hannun jarin naira biliyan 16, abin da ya sani hannun jarin naira biliyan uku ne da doriya. Ya ce kamfanin saka jari na jiha kai tsaye yana bayar da bayani ne a fadar gwamnati ba a karkashin ma’aikatar kudi ba wadda ya yi wa Kwamishina daga Yuni 2019 zuwa Maris 2022.
- Manufar “Sabon Karfin Samar Da Hajoji Da Hidimomi Masu Karko” Za Ta Samar Da Ci Gaban Da Duniya Ke Muradi
- Ambaliya: Gidauniyar Tunawa Da Sardauna Ta Bai Wa Maiduguri Tallafin Miliyan 20
Ya ce shugaban kamfanin saka jari ya fada masa cewar, baki daya hannun jarin na naira biliyan uku ne da doriya wadanda aka hade su a waje daya a 2017 aka kuma dauke su daga ma’aikatar kudi aka mayar da su a karkashin kamfanin saka jari, ya kuma ce ba ya da masaniyar ko an sayar da hannun jarin.
Ya ce “A lokacin cutar korona a 2020 wadda tattalin arzikin Nijeriya da duniya baki daya ya tabarbare, an samu karancin kudaden kason wata- wata daga gwamnatin Tarayya da karancin haraji, kuma an ba mu umurnin fara biyan mafi karancin albashi na naira dubu 30.”
Dasuki ya bayyana cewar, a bisa wannan dalilin ne Tambuwal ya bai wa kamfanin saka jari umurnin ba su naira biliyan biyu wadanda da farko aka ba su naira biliyan 1, daga baya aka ba su naira miliyan 500 wadanda aka saka a asusun babban akawun gwamnati domin gudanar da muhimman ayyukan raya jiha, biyan albashi da sauransu.”