Tsohon mai neman takarar gwamna a jam’iyyar APC a zaben fidda da gwani na 2023, Faruku Malami Yabo ya sauya sheka daga APC zuwa PDP a Jihar Sakkwato.
Yabo, ya bayyana cewar ya koma PDP wadda ke da kyakkyawan tsarin dimokuradiyya, mutunta jama’a da hadin kai tare da karbuwa ga kowa.
- Mutum 18 Sun Kone Kurmus A Hatsarin Mota A Bauchi
- Ba Buhari Ne Sanadin Jefa ‘Yan Nijeriya Cikin Talauci Da Yunwa Ba – Ngige
Haka ya godewa al’ummar yankin kan goyon bayan da suke ba shi tare da kara kira gare su da su kara bayar da cikakken goyon baya ga nasarar PDP a dukkanin matakai.
Ya bayyana hakan ne a gangamin yakin neman zaben PDP a Karamar Hukumar Yabo, inda Gwamna Tambuwal ya karbe shi tare da dubban magoya bayansa.
Da yake jawabi ga mahalarta taron, Tambuwal, ya bayyana cewar sun zo Yabo ne domin nuna godiya saboda amincewar Faruk Yabo na shiga PDP.
“Wannan ranar muhimmiya ce a cikin ranaku masu tasiri ga dimokuradiyya a Sakkwato.
“Dan uwa mun jima muna tsammanin shigowarka wanda babban ci gaba ne ga zaben da ke gabanmu.”
“Ranar yau ta nuna manuniyar samun nasarar PDP a Sakkwato da Nijeriya baki daya,” in ji Tambuwal.