Tsohon shugaban kwamitin din-din-din na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin Wu Bangguo ya rasu yana da shekaru 84 a yau Talata da misalin karfe 4:36 na sanyin safiya agogon Beijing.
Wu Bangguo, ya taba zama mamban ofishin siyasa kuma sakataren sakatariyar kwamitin kolin JKS karo na 14, da mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS karo na 15, zaunannen memban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS karo na 16 da na 17. Haka kuma tsohon mataimakin firaministan kasar, kana shugaban kwamitin din-din-din na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 10 da na 11.
Kwamitin kolin JKS da kwamitin din-din-din na majalisar wakilan jama’ar Sin da majalisar gudanarwar kasar da kwamitin kasa na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa, sun fitar da sanarwar mutuwar, inda suka bayyana marigayi Wu Bangguo a matsayin amintacce mai kishin jam’iyyar kuma dan juyin juya hali, dattijo, kana shugaba a jam’iyyar da ma kasar. (Fa’iza Mustapha)