Tsohon mataimakin gwamnan jihar Gombe, Tha’anda Jason Rubainu tare da wani jigo na jam’iyyar PDP, Hon. Jerry Joseph Damara, sun fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
An karɓe su tare da wasu fitattun ƴan jam’iyyar PDP, mafi yawa daga yankin Gombe ta Kudu, a fadar gwamnati da ke Gombe, inda Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya tarɓe su. Rubainu ya kasance mataimakin gwamna a lokacin mulkin tsohon Gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo daga 2011 zuwa 2015, yayin da Damara ya bayyana shigarsa APC a matsayin babban sauyi na siyasa a jihar.
- Yadda Wani Mai Unguwa Ya Yi Wa ‘Yar Shekara 12 Fyade A Gombe
- Bauchi Da Gombe Sun Koka Kan Jinkirin Aikin Haƙo Mai Na Kolmani
Damara, wanda aka san shi a matsayin ɗan kasuwa kuma mai taimakon jama’a, ya ce manufar sa ta sauya sheka ta samo asali ne daga gamsuwa da salon shugabancin Gwamna Yahaya, musamman a fannin ayyukan gine-gine da tsaro. Ya ƙara da cewa bai shigo shi kaɗai ba, ya zo da magoya baya da dama, tare da alƙawarin cikakken goyon baya ga jam’iyyar APC.
A nasa jawabin, Gwamna Yahaya ya bayyana wannan sauya sheƙar a matsayin rana ta musamman ga jam’iyyar APC a Gombe da ma ƙasa baki ɗaya. Ya ce samun goyon baya daga Gombe ta Kudu abin da ya ke da matuƙar muhimmanci ne, musamman ganin jam’iyyar bata yi nasara sosai a can a zaɓen da ya gabata ba.
Ya kuma yaba wa Shugaban ƙasa Bola Tinubu bisa ƙirƙirar yanayin siyasa da tattalin arziƙi mai kyau, tare da jinjina masa kan cire tallafin mai da ya kira matakin jarumta da ya taimaka wajen daidaita tattalin arziƙin ƙasa. A kan ayyukansa a jihar, Gwamnan ya ce, “Ayyukan da muke yi a Gombe abubuwa ne da ya kamata an yi su shekaru 30 da suka wuce,” yana mai tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta hanzarta ƙara yin abubuwan ci gaba da haɗa kan jama’a.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp