Henri Konan Bedie, tsohon shugaban kasar Cote d’Ivoire, kuma fitaccen dan siyasa da ya dade yana rike da madafun iko a kasar da ke yammacin Afirka shekaru da dama ya rasu yana da shekaru 89 a duniya.
Bedie ya zama shugaban kasa daga shekarar 1993 har zuwa lokacin da aka hambarar da gwamnatinsa a shekarar 1999, daga baya kuma ya fafata da abokin hamayyarsa na siyasa, Alassane Ouattara, a zabe a shekarar 2020 yana da shekaru 86 a duniya.
- Badakalar Biliyan 1.3: EFCC Ta Maka Sule Lamido Da Wasu A Kotun Koli
- Masu Zanga-zanga Sun Karya Kofar Majalisar Wakilai Kan Cire Tallafin Man Fetur
Har yanzu ba a san musabbabin mutuwar Bedie ba.
An girmama shi musamman saboda sa hannu a cikin gwagwarmayar manufar “Ivoirite,” wanda ya shafi ainihin dan Ivory Coast.
Batun ya kara tada jijiyar wuya tsakanin wadanda ke daukar kansu ‘yan asalin kudu da gabas, kuma da yawa daga cikin ma’aikatan kasashen waje daga kasashen makwabta sun dade a arewacin kasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp