Tsohon shugaban jam’iyyar PDP kuma tsohon ministan noma daga 2015 zuwa 2019, Audu Ogbeh, ya rasu a ranar Asabar, 9 ga Agusta, yana da shekaru 78 a duniya, kamar yadda iyalinsa suka tabbatar.
A cikin wata sanarwa, iyalan sun ce: “Ya rasu cikin kwanciyar hankali, ya bar mana gado na gaskiya, hidima da jajircewa ga kasa da al’umma. Mun sami kwanciyar hankali daga yadda ya shafi rayuka da kuma yadda ya kafa misali.”
- Ko Nawa Za A Bani Ba Zan Iya Fitowa A Matsayin Kwarto Ko Dan Daudu A Fim Ba -Dan Asabe Olala
- Jihar Gombe Za Ta Rungumi Shirin Farfado Da Noman Auduga Na Gwamnatin Tarayya – Inuwa
Iyalan sun bayyana cewa za a sanar da yadda za a gudanar da jana’izarsa a nan gaba, tare da godewa abokai, da abokan aiki. Sun kuma roƙi a basu dama domin yin jimamin rasuwar baban nasu.
Rahoton LEADERSHIP ya nuna cewa Ogbeh, wanda ya shahara a siyasa, rubuce-rubuce da aikin gona, ya shugabanci PDP daga 2001 zuwa 2005 kafin ya zama minista a gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp