Tsokacin mu na yau zai yi duba ne game da abin da ya shafi Auren Bazawara da kuma Macen da ta girmi mijin da za ta aura.
Sau da dama ana samun namijin da bai taba aure ba, yana son auren macen da ta taba aure, ko ta fi shi shekaru, sai dai kuma wani sa’in akan sami tsaiko ta fannin iyayen saurayin ganin cewa shi yaro ne da bai taba aure ba, sai su yi yunkurin hanawa ko da kuwa masoyan suna son junansu.
Shin auren Bazawara ko matar da ta girmi saurayi yana da fa’ida ciki?, idan kai ne ko kece za ki/ka iya?. Dalilin haka ya sa wannan shafi ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiyansa inda suka bayyana nasu ra’ayoyin kamar haka:
Binta Umar Abbale daga Jihar Kano:
Auran Bazawara abu ne mai asali, idan an yi la’akari da cewa Annabi Muhammadu (S.A.W) wanda ya fi kowa a duniya da bazawara ya fara a matsayinsa na saurayi wanda bai taba aure ba amma ya auri bazawara wato sayyada Khadija wacce ta girme masa a shekaru, a tarihi cewa sun zauna lafiya da juna ma’aiki (S.A.W) ya ji da dadin zama da ita har tayi wafati kuma ita ce uwar ‘ya’yansa, saboda haka auran Bazawara asali ya dauko, kuma sunnah ce mai karfi.
Akwai fa’ida ga auran Bazawara misali; Saurayin da bai taba aure ba ya auri Bazawara wacce tayi aure har ta haihu, fa’idar auran Bazawara shi ne; Ta san rayuwa tayi zamantakewar aure, ta san kalubalan dake faruwa za ta iya jurewa ba kamar budurwa ba da ba ta san komai ba. 2; Bazawara za ta kula da miji ta fannoni daban-daban.
Tarbiyyar yara, kula da miji, Kula da shimfidar miji, Hakuri da yau da gobe, Tarairaiyar Miji da kalami mai dadi da dai sauransu. Duk da cewa budurwar ma za ta iya wadannan abubuwan dana lissafa amma ba kamar Bazawara ba.
Eh babu Laifi don Namiji ya auri wacce ta girme shi ko kuma Mace ta auri wanda ta girma da shekaru duk hakan ba laifi bane, abin da dai ake bukata a nan shi ne; zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin zaman auran. Shawara ta anan shi ne; idan Namiji ya ga wacce ya ke so kuma ta girme shi ko kuma Bazawara ce to ya toshe kunnuwansa ga barin jin surutai irin na jama’a ya duba abin da Allah ya halasta ya kuma sa a ransa cewa auran da zai yi alkairi ne a gare shi.
Yareema Shaheed (Dan Amar) daga Jihar Kano:
E! Auren macen da ta girmi mutum ko Bazawara akwai babban fa’ida domin mutum zai fi samun cikakken kulawa kuma ba za ta dinga yi masa yarinta ba kuma za ta yi masa biyayya sosai.
Fa’idojin da auren Bazawara ko Matar da ta girmi mutum ga su kamar haka; Tarairaya da tsafta, da sanin ya kamata, da kiyaye dokokin miji tare da kiyaye duk wani abu da tasan mijin baya so. E! Zan iya auren wacce ta girme ni ko Bazawara domin dama abin da ake so a zaman aure shi ne zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ina ba da shawarar da komai ya zo mana a rayuwarmu mu dinga hakuri mu karbeshi hannu bibbiyu.
King Abdul daga Jihar Kano:
Da fa’ida auren Bazawara, haka za da fa’ida auren matar da ta baka shekaru. Fa’ida da auren bazawara yake da shi shi ne; ana samun soyayya mai karko, auren bazawara indai da so sannan hankali yana kwantawa sosai a auren, bazawara, hasali na san da za a yi gasar soyayya tsakanin ‘yammata da zawarawa na san ba sai na fad’i su waye za su ci gasar ba.
(AUREN MATAR DA TA GIRMEKA); tabbas yana da fa’ida ka!i ni a ganina auren ta ya fi ka auri yarinya ko bazawara. Ni zan iya auren matar da ta girme ni. Shawarata su rike alkawari su zauna da su da amana.
Aisha Musa ‘Yankara:
Sosai ma kuwa, Akwai fa’ida a auren bazawara da wacce ta girmi mutum, ita bazawara ta taba aure ta san wasu daga cikin kalubalen auren da kuma farin cikin auren ba za ta so idan ta kuma wani auren ta fito ba to anan ne za ki ga kokarin kyautatawa mijin take ta yadda za ya kasance yana mai farin ciki da auren nata.
Sannan idan muka duba tarihi za mu ga cewa; Manzon Allah (S.A.W) ya fara auren wacce ta girme shi kuma bazawara kin ga kenan akwai fa’ida. Fa’idar shi za ka samu kulawa, kiyayewa, takatsamtsam, da sauransu. Sosai ma kuwa zan iya aure, Shawara su nemi zabin Allah.
Maryam Rabi’u Musa, Jihar Kano:
Sosai kam! akwai fa’ida a ciki mai yawa. Fa’idar ita ce; tunani mai kyau da kuma hangen nesa. Eh zan iya auran wanda na fi shekaru, ko saurayin da bai taba aure ba, shawarata gare su ita ce; su zauna lafiya da abokan zamansu, kar dan mace ta auri yaro kuma ta kasa yi masa biyayya, ko kuma shi mijin ya rinka dauka alfarma yayi wa matar.
Muhammad Bamalli Inkiya (Bazazzage mai iyali):
Auren bazawara idan har mutuniyar kirki ce ko wacce ta girme ka yana da amfani domin kuwa ta san abubuwa da yawa na rayuwa kuma ta fahimce su
Bazawara ta yi aure ta san yadda ake kula da miji, Wacce ta girme ka kuwa, Hausawa na cewa; abin da babba ya hango yaro ko ya taka tsani ba zai hango ba, domin haka ta san abubuwa da yawa da kai baka sani ba.
Fa’idar auren su shi ne su kasance mutanen kirki kawai, Tabbas zan iya auren bazawara matukar mutuniyar kirki ce, ko kuwa aka yi sa’a mun taba yin soyayya da ita tana budurwa, Shawara ta ga masu fuskantar hakan shi ne; su yi duba da halaye ba shekaru ko kyawu ba.
Muhammad Karim daga Jihar Kaduna Nijeriya:
Auren Bazawara ko macen da ta girmi mutum akwai fa’ida sosai. Saboda ko yanayin hankalinsu, da budurwa masu kananun shekaru ba zai zama daya ba, kuma ko Manzon Allah (SAW) Lokacin da ya auri Nana Khadija ta girme shi. Idan ni ne tabbas zan iya auren bazawara, ko wacce ta girme ni, muddin muna kaunar junanmu zan iya aurenta ba wani matsala bane, tun da auren soyayya ake bukata da kuma fahimtar juna kuma ko addini ya halasta ka aura. Shawarar da zan bawa masu fuskantar hakan shi ne; duk halin da mutum ya riski kanshi ya kwantar da hankalinsa sannan ya yi wa Allah godiya saboda ko wani bawa baya iya kaucewa kaddarar sa.
Fadila Lamido daga Jihar Kaduna:
Auren mace wacce ta fi ka shekaru yana da fa’ida, Na farko za ka samu ladan sunna, domin yin koyi ne da fiyayyen halitta, sannan akwai yiyuwar samun ingantacciyar rayuwar aure matukar dai akwai kauna a tsakani, saboda ita ta zauna da wasu mazan ta san rayuwar aure, ta san me namiji yake so ta san abin da baya so, ta sami kwarewa ta bangarori daban-daban, ko da ba ta taba aure ba a baya shekarun da ta yi a rayuwar ta zai sa ta ga abubuwa kala-kala na rayuwa, wada za su zamar ma ta darasi a zamantakewar aure nan gaba, bazawara ta fi budurwa sanin makamar sirrin zamantakewar aure musamman ma in ta sami saurayi wato wanda ta girma, matukar akwai kyauna fa, bazawara tana da hakurin zamantakewa fiye da budurwa, bazawara ko wacce ta fi ka shekaru ta san halayen iyayen miji da yadda ake zama da su, sabanin budurwa, sai dai kuma ni gaskiya a ra’ayina ba zan auri namijin dana girma ba, duk da cewa ba wani aibu bane, amman a ra’ayina ba zan taba auren namijin da na girma ba koda ace kuwa ban taba aure ba, shawarata ga wadda suka samu kansu a cikin irin wannan yanayin sutabbatar akwai kauna me karfi a tsakaninsu kafin auren bawai so ba.
Nana Aicha Hamissou, Maradi Jamhuriyar Nijar.
Assalamu alaikum. Fatan alheri da ‘yan’uwa da abokan arziki. Da fatan mun wayi garin juma’a cikin koshin lafiya. Iyayena ba zan gaji da gai da ku ba a kowanne lokaci. Sakon barka da juma’a ga Æ™awayen amana Hawaou Mantao, Fatchima, Yasmina, Rayanatou, Mouchitahida & my Harira.
Ina gai da ‘yan’uwana Marubuta maza da mata ba sai wane da wane ba.